Sojoji sun aika da Kachalla barhazu tare da wasu manyan kwamandojin ƴan ta’adda


Shelkwatar tsaro ta ƙasa ta tabbatar da kashe wasu fitattun kwamandojin ‘yan ta’adda hudu a hare-haren da aka kai ta sama cikin mako guda.
Ƴan ta’addan su ne Machika, Haro, Dan Muhammadu da Ali Alhaji Alheri, wanda aka fi sani da Kachalla Ali Kawaje.
Daliy Nigerian hausa na ruwaito Darakta mai kula da ayyukan yada labarai na tsaro, Maj.-Gen. Edward Buba ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Asabar a Abuja.


Buba ya ce Machika babban kwararre ne mai haɗa bama-bamai ne kuma kanin fitaccen dan ta’adda (Dogo Gide) ne, yayin da Haro da Dan Muhammadu suka kware wajen yin garkuwa da mutane.
Ya ce wani farmakin hadin gwiwa da sojojin sama da na kasa suka kai a ranar 11 ga watan Disamba ne yai sanadiyar kashe Kachalla Kawaje, wani fitaccen shugaban ‘yan ta’addan da ke da alhakin sace daliban Jami’ar Tarayya ta Gusau, Zamfara.
Ya kara da cewa an kashe Kachalla ne a karamar hukumar Munya ta Nijar tare da wasu yaran sa da dama.
A cewarsa, sojoji sun kisa cimma sauran ƴan ta’addan, yayin da wasu kuma za su fuskanci irin wannan halin nan gaba kadan.
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)






