Labarai

Wata mata ta fadi yadda taka hada jininta da zobo ta sayarwa mutane – inji wata mata mai Cutar kanjamau

Advertisment

Wata mata da har yanzu ba a tantance ko tana dauke da cutar kanjamau ta HIV ba, ta ce tana hada jininta a cikin ruwan zobon da take sayarwa domin akara samun wasu mutanen da cutar ta kama

Matar ta bayyana hakan ne a wani shirin gidan rediyon Wazobia FM, MarketRunz a daren Laraba

Mai gabatar da shirin ya nemi masu sauraro su kira su shaida abin da suke yi a kasuwa wanda mutane ba su sani ba da kuma abin da ba sa alfahari dashi.

Mai sayar da zobon ta ce, “Na je asibiti wata shida da suka wuce, sai aka ce mini ina da cutar kanjamau wato HIV.

“Ba ni da kuɗin magani don haka na yanke shawarar cewa ba zan mutu ni kaɗai ba. Na fara hada jinina da zobo da nake yi in sayarwa da mutane don suma suka mu don mukara yawa.

Ina zukar jinina da sirinji in hada shi a zobo. A da ni ma’aikaciyar jinya ce amma da aka tabbatar min da ina da cutar kanjamau, sai na daina zuwa Aiki.

“Ban ji dadin abin da na yi ba amma ina farin ciki cewa ba zan mutu ni kadai ba.”

“Na yi wata shida yanzu ina addu’ar Allah ya gafarta min.”

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button