Ina Rokin Allah Ya Dauki Rayuwata A Dakin Mijina -Tsohuwar Jaruma Fati Ladan
Tsohuwar jaruma a masana’antar Kannywood, Hajiya Fati Ladan, ta bayyana dalilin da ya sa take har yanzu a gidan mijinta duk da cewar ana cewa ‘yan fim ba su cika zaman aure ba, kuma ta yi fatan Allah ya kashe ta a dakin mijinta.
Fati ta yi wadannan kalaman ne a hirar da ta yi da manema labarai dangane da cikar ta shekara goma cur a gidan aure a gidan mijin ta a Kaduna.
Alhaji Yerima Shettima, shugaban Kungiyar Tuntuba ta Matasan Arewa (Arewa Youth Consultatibe Forum), shi ne mijin ta.
Jaridar Leadership hausa na ruwaito, Fati da Yerima dai su na da ‘ya’ya biyu a tsakanin su, A’isha Humaira da Muhammad Shafi’u, kuma su na zaune ne a Kaduna. Fati ita ce amarya a cikin matan sa biyu.
Da take amsa tambayoyin yan jarida Fati ta bayyana matukar godiyarta ga Allah (S.W.T.) da ya nuna mata wannan lokaci inda ta bayyana shekara goma ba kwana goma ba ne.
Ta kara da cewar zaman aurenta na tsawon shekaru 10 ba wani sirri ba ne illa kawai hakuri da soyayya saboda soyayya idan babu hakuri, sai ka ga kuma ba za a kai ga cimma inda ake so a kai ba.
Saboda a duk lokacin da mutum ya ce zai yi abu, musamman aure, to ina tunanin ba wasa ya je yi ba, aure abu ne wanda in har ka yanke hukuncin cewa za ka yi shi, ka san da sanin cewa ibada za ka je ka yi ba sharholiya ba.
A lokacin da na yanke shawarar zan je in yi aure, na sanya wa zuciya ta cewa zan je in zauna, ibada zan yi wannan abin da na sa wa rayuwa ta ya sa ban fuskanci wani kalubale dangane da zaman aure na ba ko in ji ina kewar wani abu ba.
Kuma miji na ya na ba ni goyon baya dari bisa dari a dukkan abin da na ce zan yi in dai bai saba wa addini na ba da al’ada ta zai ba ni goyon baya.
Hakan ne ya sa na maida shi kamar aboki a wuri na, shi kuma ya maida ni kawa a wurin shi duk abin da za mu yi, mu na yin shi tare da ni da shi ban yi ‘missing’ din wani abu ba, gaskiya, saboda duk abin da na ke nema ina samu a wurin miji na.
Da take amsa tambaya akan ko tana alfahari da kasancewarta tsohuwar jarumar fina finan Hausa, Fati Ladan ta ce a duk lokacin da na wuce har yanzu, za ka ji ana cewa,ba ku gane ta ba, ai ita ce Fati Ladan, tsohuwar jarumar nan,wasu da dama za su zo su yi hotuna da ni, kuma na san cewa in ba albarkacin fim ba, babu yadda za a yi a san ni to ina alfahari da wannan kwarai da gaske.
Kamar yadda aka yi mana kudin goro, aka ce ba mu zaman aure, ba haka ba ne. ni a tunani na ba auren ‘yan fim kadai ke mutuwa ba, amma da yake mu an san mu, dole za a rika yi mana kudin goro ana cewa ba mu zaman aure, amma mu na zaman aure.
Fati ta kuma bayyana cewar a halin yanzu ba ta sha’awar harkar fim “amma maganar in ji ina sha’awar harkar fim, ba na yi gaskiya,daga lokacin da na ce na hakura, na yi ritaya na aje, ko kuma na ba shi baya, ba wai don ba shi da wani abu ba aure na fuskanta, kuma ina fata Allah ya kashe ni a dakin miji na, shi ne fata na.
Daga karshe Fati Ladan ta bayyana cewa tana yiwa masoyanta fatan Alheri kuma tana mika sakon godiya ta musamman a kan soyayya da su ke nuna mata a lokacin da ta ke waje da kuma yanzu da tayi aure.
A ranar 20 ga Disamba, 2023 in Allah ya kai mu Fati Ladan da mijin ta Yerima Shettima za su cika shekara goma cur da aure an daura auren su ne a ranar Juma’a, 20 ga Disamba, 2013 a kofar gidan su Fati da ke Unguwar Sarki, Kaduna.