Labarai

KWADAITARWA GA MATA: Ku rika bari mazajen ku na sumbatar nonon ku akai akai – Inji kwararriyar Malamar UngoZoma

Wata kwararriyar malamar Ungozoma Roseline Oladimeji, ta shawarci mata su rika bari mazajen su na tsotsar maman su musamman a lokacin da suke da ciki.

Malama Oladimeji ta bayyana haka ne a wajen taron makon shayarwa da aka yi a jihar Legas, Najeriya.jaridar Leadership hausa na ruwaito.

” Baya ga kara dankon soyayya da zai dada karfi a tsakanin ma’auratan, idan maigida na tsotar mamar matar sa yakan sa bakin nonon ya fito sannan yayi karfin da idan jariri ya zo duniya zai ji dadin tsotsa da kyau.

” Haka kuma ana iya saka man shafawa a bakin maman da dare idan za a yi barci. A karshe ta yi kira ga mata da su rika shirin maman su suna gyara su domin shirin shayar da jariri a lokacin da suke da ciki.

Kungiyar kiwon lafiya ta duniya WHO da asusun UNICEF sun yi Kira ga gwamnatocin duniya da su cigaba da wayarwa mutane kai game da mahimmancin shayar da jarirai nonon uwa na tsawon akalla watanni shida bayan haihuwa.

Kungiyoyin sun yi wannan kira ne a shafinsu na yanar gizo a makon wayar da Kan mutane mahimmancin shayar da jarirai nono ta duniya da ake yi a kowace shekara daga ranar 1 zuwa 7 ga watan Agusta.

A jawaban da suka yi shugabanin UNICEF Henrietta Fore da na WHO Tedros Ghebreyesus sun ce shayar da jariri nono na da mahimmanci saboda nono na dauke da sinadarin dake inganta kiwon lafiyar yaro musamman na kariya daga daga kamuwa da cututtukan dake kisan yara kanana.

Shugabanin sun ce yin haka zai taimaka wajen ceto rayukan yara 820,000 dake mutuwa duk shekara a duniya.

Mahimmancin shayar da jariri nonon uwa

Likitoci sun bayyana shayar da jariri nono zalla musamman na tsawon watanni shida ko Kuma fiye da haka abu da ke kara lafiyar jarirai.

Ma’aikatar kiwon lafiya ta bayyana cewa kasa da kashi 24 bisa 100 na jarirai ne suke samun shayarwar wayen su wato nono na tsawon watanni shida a kasa Najeriya.

Jami’in ma’aikatar kiwon lafiya Chimay Thompson ya fadi haka, sannan ya kara da cewa rashin yin haka na daya daga cikin dalilin dake kara mace-macen yara da mata.

” Shayar da yaro ruwan nono zalla na tsawon watanni shida hanya ce dake taimaka wa wajen inganta lafiyar yaro da na uwa.” Inji Thompson.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button