Kannywood

Babban burina a rayuwa shine na gani a dakin Aure – khadija Muhammad

A daidai lokacin da wasu suke yayata maganar cewa jarumai mata a masana’antar Kannywood basu fiye son zaman aure ba, Jaruma Khadija Muhammad ta karyata wannan zance kwata-kwata inda ta tabbatar da cewar wannan magana sam babu kamshin gaskiya a cikinta domin kuwa a halin yanzu bata da wani buri da ya wuce ta yi aure ta kuma tare a gidan mijinta.

Jarumar ta yi wannan jawabi ne a wata hira da ta yi da BBC a cikin shirinsu na daga bakin mai ita inda ta bayyana batutuwa da dama da suka dangance ta,kama daga karatunta shigowarta masana’antar Kannywood da sauransu.

Leadership hausa ta tattaro cewa Jaruma Khadija ta ce ita haifaffiyar garin Kano ce a unguwar Kabuga,anan Kabuga ta yi karatun Firamare da Sakandire kafin ta wuce makarantar gaba da Sakandire ta Usman Danfodiyo Unibersity da ke da reshe a Kwalejin Ilimi ta Jihar Kano, ta kuma bayyana cewar ta taba yin aure amma yanzu ba su tare da mijin nata.

Da ake tambayarta a kan ta yaya ta shigo harkar fim, jarumar mai shekaru 30 ta bayyana cewar akwai da dama daga cikin yan unguwarsu ta Kabuga da suke cikin wannan harka ta Kannywood hakan yasa suke yawan shigowa Kabuga domin daukar fina finansu, da haka ne har sha’awar shiga wannan harka ta kama ta har ta nemi shawarar yan uwa da abokan arziki, bayan ta tuntubi gida sai aka amince mata ta fara fim, indata fara fitowa a wani shiri mai suna Dr Bahijja.

Tun daga wannan lokacin Khadija ta fito a manya manyan fina finai a masana’antar ta Kannywood da suka hada da Alaka, Gidan Sarauta da sauransu inda ta bayyana fim din A Duniya da ta fito a matsayin wanda tafi so domin kuwa anan aka fi saninta in ji ta,amma a halin yanzu bata da wani buri da ya wuce tayi aure ta tare a dakin mijinta.

Daga karshe Khadija ta bayyana cewar akwai bukatar jarumai da mahukunta a wannan masana’antar ta Kannywood su samu hadin kai wanda shi kadai ne abinda zai samarwa masana’antar cigaba mai dorewa,inda ta tabbatar da cewa a duk wata tafiya wadda babu hadin kai a tsakanin wadanda suke cikinta babu ta yadda za’a yi wannan tafiya ta ci gaba domin kuwa hadin kai shi ne kashin bayan ci gaban kowace irin tafiya.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button