Batanci ga Annabi: An kafa sharudda 4 a kan mika Rahama Sadau gaban kotu
=>Wani lauya mai suna Lawal Muhammad Gusau ya gabatar da takardar korafi ga Sifeta janar na ‘yan sanda
=> A takardar, ya mika korafinsa a kan jaruma Rahama Sadau, akan hotunan da ta wallafa da suka janyo suka ga manzon Allah (S A W)
=> Lauyan, ya gindaya sharudda 4 ga jarumar, wadanda yace wajibi ne ta cika su, tunda za a yi shari’ar ne a kotun musulunci
Bayan gabatar wa da sifeta janar na ‘yan sanda takardun korafi a kan kalaman batancinda aka yi wa manzon Allah (S A W) da hotunan Rahama Sadau suka janyo, kotu ta gindaya mata sharudda 4 da zata cika.
A ranar Litinin, NewsWireNGR sun ruwaito yadda hotunan Rahama Sadau suka janyo cece-kuce a kafafen sada zumuntar zamani, wadanda suka kai ga jarumar ta cire hotunan kuma ta bayar da hakuri.
Jarida Legithausa sun wallafa a sahafin cewa da yawa daga musulman arewacin Najeriya sun nuna yadda hotunan suka kawo suka ga arewa, musulunci da imaninta. Wasu kuma suka yi ta kokarin kareta.
Amma a wata takarda da wani lauya, Lawal Muhammad Gusau, ya rubuta a ranar Asabar, ya ce dole jarumar Kannywood din ta cike sharudda 4.
1. Wajibi ne lauyanta ya zama musulmi. Don ya fahimci hukuncin kotun shari’ar musulunci. Don za a yi amfani da hadisi da Al’kur’ani mai girma wurin yanke hukunci.
2. ‘Yan sanda za su yi aikinsu na kai ta kotun shari’a ne saboda hakkinsu ne, don a tabbatar da binciken a kan ta.
3. Sannan manyan malamai kamar Sheikh Ahmed Mahmoud Gumi da ke Kaduna, Sheikh Ahmed BUK daga Kano, Sheikh Kabir Haruna Gombe daga Gombe, Sheikh Nura Khalil daga Abuja da Sheikh Ali Isa Fantami, ministan sadarwa, sune malaman da za su bayar da fatawa a kan sukar manzon Allah Muhammad (SAW).
4. Mun jinjina wa lauyoyin arewa da basu shiga cikin sabon da wani Aminu Sherif da Umar Faruk suka yi ba. Sannan ba mu bukatar ganin wani lauya mazaunin Kaduna ya saka baki a cikin lamarin Rahama Sadau.