Yadda Na Ke Rera Waka Ba Tare Da Karantawa Ba — Malam Yahaya Makaho
MALAM Yahaya Usman, wanda aka fi sani da Malam Yahaya Makaho a fagen wakoki na Hausa, makaho ne wanda ba ya gani ko daya. Faifan sa mai suna ‘Haka Allah Ya So’, wanda ya fito kwanan baya (inda a ciki ya yi wakoki da su Aminu Ala da El-Mu’az Birniwa), ya burge mutane matuka. Ganin cewa makaho ne, mutane sun yi ta mamakin yadda wannan fasihin ya ke rera wakoki masu ma’ana da daukar hankali. Shin haddacewa ya yi ko kuwa dai ya na karantawa ne? Wakilin mu ya yi tattaki har wurin aikin sa a Kaduna ya yi hira da shi, inda ya warware masa zare da abawa game da yadda ya tsinci kan sa a harkar waka da kuma sauran abubuwan da su ka shafi rayuwar sa.
FIM : Ka fada wa masu karatu cikakken sunan ka da tarihin rayuwar ka a takaice.
YAHAYA MAKAHO : A takaice, suna na Yahaya Usman, amma an fi sani na da Malam Yahaya Makaho. Kuma na samu wannan matsalar ne sanadiyyar wata matsala da ta ke tare da ni na rashin gani. An haife ni a shekarar 1983 a Karamar Hukumar Giwa (Jihar Kaduna). Na yi makarantar allo a Kaya da Fatika. Na shigo garin Kaduna a shekarar 2003 da zummar zan zo in yi wata sana’a da zan dogara da kai na amma a wannan lokacin sana’ar da na ke yi, sai ta zama ba sana’a ba ce da za ta iya dauka na ko kuma ta zama dorarra a tare da ni. Tun farko ni na iya sana’o’i daban-daban, wanda a kauye na ke jarrabawa, don haka na yi tunanin idan na shigo gari zan samu jarin da zan ci gaba da yi, sai kuma hakan ya gagara, sai na buge da sana’ar waka.
FIM : Malam Yahaya, ina maganar karatun zamani?
YAHAYA MAKAHO : Ka san lokacin baya, mu musamman Arewa, akwai karancin maida hankali a kan al’amarin shi. An fi maida hankali a kan karatun allo a baya saboda shi mu ka fi yarda da shi, shi iyayen mu su ka tashi a ciki. Amma ko a lokacin ni ina bin yara mu je makarantar firamare. Sai wani malami mai koyar da Arabiyya, shi ya fara kiran mahaifi na ya ce masa bai kamata a sa ni a makarantar boko ba, saboda makarantar allo ya kamata na yi. Wannan dalilin ya sa ban yi karatun zamani ba.
FIM : Ya aka yi ka tsinci kan ka a harkar waka?
YAHAYA MAKAHO : Kasancewar ni mutum ne da tun farko ina da kokarin duk abin da zan yi na rungumi wata da za ta iya zame min mafita, kafin na fara waka kuma na yi sana’o’i daban-daban. Da na bar sana’o’in na shigo gari, sai ya zama sana’ar da zan yi a kauye ba lallai ba ne su yi tasiri a cikin gari. Wadda na ke tunanin za ta yi tasiri a cikin garin kuma ita na fara, sai na ga ba za ta bulle da ni ba. Ina cikin neman mafita ne da shawarwarin mutanen da na ke tare da su, sai wani mawaki ya fada min yadda zan yi in shigo harkar waka. Ya ci gaba da ba ni shawarwari. Duk da haka dai ban fahimci abin da ya ke nufi ba sosai, sai da na shiga situdiyo. A lokacin ne na gane ya na yi min maganar dango da kafiya: abin da ka fara da shi ana so ka karkare da shi. Idan dango uku ka ke yi, na hudu sauka. To duk wakar haka za ta zama.
FIM : Kasancewar yanzu yawancin mawaka idan su ka tashi yin waka rubutawa su ke yi, ga ka makaho, ta ya ka ke yin naka?
YAHAYA MAKAHO : Alhamdu lillahi! Ni na kan ba kai na lokaci, kamar yadda masu rubutu su ke ba kan su lokacin tunani a tuno kalma a rubuta. Ni kuma maimakon rubutun in na yi nazarin kalmar, sai na rubuta ta a cikin kwakwalwa, sai ya zamana a cikin kwakwalwa na ke aje duk wani abu da zan nema in yi amfani da shi cikin waka.
FIM : Bangaren matan da ke yi maka amshi kuma fa?
YAHAYA MAKAHO : Shi amshi wani abu ne, wanda yadda ake yi wa kowa haka ake yi min. Mata tunda ba su za su kirkira ba, kuma in har na riga na ce zan yi wakar misali duk abin da na fada shi za ta fada, ka ga wannan wani abu ne mai sauki.
FIM : Kasancewar ka makaho, ka taba yin bara a baya, kafin ka yi sana’o’in da ka ce ka yi kafin ka fara waka?
YAHAYA MAKAHO: A farkon shigowa na Kaduna bara na shigo na yi. Shi ya sa ka ji na ce “wata sana’a da na fara na ga ba za ta bulle da ni ba”. Farko bara na shigo yi, kuma dalili na na bara, lokacin wani bawan Allah ya rika ba ni shawara cewa in na fara bara, wasu sai sun ci abinci karkashi na, ba ma ni ba. Don haka shi ya kwadaita min baran, na ji baran na ke so na yi, kuma na yi. Amma daga baya sai na ga barar nan ta na hana ni mu’amala da ’yan’uwa na, saboda ita ta na da cin rai, kullum in ka samu dari uku, tunanin ka gobe za ka samu dari hudu ko biyar, tunda ba sana’a ba ce ta kasawa, inda sana’a ce ta kasawa dole za ka fara tunanin ina sa ran yau zan saida kaya kala kaza, gobe zan siyo kaya kala kaza. Amma kuma bara kullum ka na tunanin daga haka sai haka ne, shi kullum ba ka da natsuwa. Wannan shi ya sa na tsane ta, ba zan iya zumunci da ’yan’uwa na ba ko kuma rayuwa cikin su kamar yadda na saba ba. Da taimakon Allah, Allah Ya raba ni da ita.
FIM : Da wace waka ka fara?
YAHAYA MAKAHO : Na fara yi wa Atiku Abubakar waka. A lokacin ya na mataimakin shugaban kasa ne, amma kuma ana sa ran zai yi takara 2007. Saboda haka lokacin sai na yi masa waka don ina kyautata zaton kila in Allah Ya hada ni da shi, zan samu damar ci gaba da waccan sana’ar da na ke yi ta sayo rediyoyi da sauran kayan wuta dai daga Legas zuwa Arewa. To, da na yi wakar kuma na ji dadin ta, mai
makon in nemi yadda zan yi in gan shi, duk da na san ko yaya zan ba zan iya ganin sa ba. To, amma da na dan kokarta da wasu na tare da shi sun san ni, sai kuma ban yi ba. Amma dai wakar sa ita na fara yi.
FIM : Yanzu wakokin da ka yi za su kai nawa?
YAHAYA MAKAHO : Gaskiya ba zan iya sanin ko wakoki guda nawa na yi ba yanzu.
FIM : Za ka iya fada mana wasu daga cikin su?
YAHAYA MAKAHO : Akwai kundin wakoki da na fitar sabo, mai dauke da wakoki guda biyar na bidiyo, na saurare kuma ya na dauke da wakoki bakwai. A cikin su akwai ‘Haka Allah Ya So’, ‘Rayuwar Duniya Iyawa’, ‘Yau Da Gobe’, ‘Nakuda’, ‘Babban Masoyi’, da sauran su.
FIM : A shekarun baya, ka taba yi wa jaruma Hadiza Aliyu Gabon waka. Me ya ja ra’ayin
kakahar ka yi mata waka?
YAHAYA MAKAHO : Wato dalili na na yi wa Hadiza Gabon waka, duk da ya ke dalili ne da ya ke sananne a wurin kowa, Allah Ya hada ni da Hadiza Gabon a kan wata gaba da na ke neman taimako kusan ko ta wace hanya, ma’ana ina neman wata hanya da zan iya dafawa ya zama ina samun taimako, wanda hakan zai iya taimako na wurin gudanar da harkoki na na rayuwa ta na yau da kullum. A lokacin sai Allah Ya hada ni da Hadiza Gabon, kuma ta kasance mai tsananin tausayi da damuwa da al’amura na. A lokacin saboda damuwa da lamura na, ba mu yin kwana uku ba mu hadu ba. Duk inda na ke za ta je ta same ni. Kuma da wahalar gaske mu hadu ba ta iya cire wani abu daga hannun ta ta ce min ga shi ba. Hasali ma ita ta raba ni da saka silifas irin na shiga bayi. A lokacin ta saya min takalmi mai tsada.
Ita ta fara saya min shadda bugaggiya, wadda a rayuwa ta ban taba sa irin ta ba. Wannan dalilin ya sa alherai daban-daban su kai ta shiga tsakani na da ita, shi ya sa ni kuma na rasa abin da zan yi in burge ta, kawai shi ne sai na yi mata waka.
FIM : Har yanzu ku na tare?
YAHAYA MAKAHO : Ka san duk zamantakewar da aka gina don Allah ba ta yankewa, sai dai in Mai rabawa Ya raba. Sai dai in abubuwa su ka yi min yawa ko kuma su ka yi mata yawa, zai zama wancan ya na can, wancan ya na can, haduwar mu zai zama da wahalar gaske. Amma ba wannan ba ne ya ke nuna ba a tare, domin duk wani abu da ya taso na alheri zan sani, za ta sani. Ka ga ko ai ana tare sosai. Kuma a shirye mu ke duk abin da ya taso na taimaka wa juna da addu’o’i ko gudunmawar jiki ko lokaci, dukkan mu za mu ba juna.
FIM : Ina maganar ubangida?
YAHAYA MAKAHO : Gaskiya ni a harkar waka, sai dai in girmama mutum saboda na ga ya kai kololuwa d azan girmama shi. Amma abin da ake nufi da ubangida, wanda ka taso a karkashin sa, ya sa ka a wata hanya ko ya koya maka wani abu, gaskiyar magana in wannan ne ba ni da shi. Amma dai akwai mutanen da na ke kallon su a matsayin iyayen gida ko na gaba da ni.
FIM : Mecece alakar ka da Aminu Ala da kuma El-Mu’az Birniwa?
YAHAYA MAKAHO : Alhamdu lillahi! Da ma mu mawaka Allah Ya yi mu da hadin kai. Za ka ga mawakan da su ka zama wani abu ba su raina na kasa da su. Aminu Ala ya na daya daga cikin wadanda su ke da kishi, in sun ga kai mawaki ne, ka na da kwazo na kirkiro abubuwan da za su amfani kasa da al’umma, Aminu Ala zai shiga gaba ya jagoranci yi maka duk abin da zai ma ya taimake ka, ya daga sunan ka a idon duniya har a san ka. Wannan shi ne ya kawo Aminu Ala a cikin al’amura na. Ba ni ba, duk wani wanda ya ga ya zo da wani abu da zai kawo ci-gaba ga kasa da kuma al’umma, Aminu Ala zai taimake shi. Haka zalika alaka ta da El-Mu’az.
FIM : Malam Yahaya ina maganar iyali?
YAHAYA MAKAHO : Malam Yahaya ya na da mata daya da yara biyu. Mata ta Lubabatu Umar, ina da Usman Yahaya, ina kuma da Sa’adatu Yahaya.
FIM : Wadanne irin nasarori ka samu a harkar waka?
YAHAYA MAKAHO : Lokacin da na zo Kaduna da silifas na zo ba tare da kowa ba, yanzu kuma ina da mata da ’ya’ya. Ka ga nasara ta farko kenan. Yanzu haka ina cikin gida na na kai na, wanda wakar ‘Haka Allah Ya So’ ce sanadiyyar samun gidan. Sannan na samu kyautar mota sau biyu, mashina sau takwas, sai kuma Keke-Napep sau daya. Wadannan su ne kadan daga cikin nasarorin da na samu. Amma babbar nasara a rayuwa Allah Ya hada ka da masoya nagari, domin su ne za su yi maka dukkan abin da Allah Ya amince za su yi maka.
FIM : Bangaren kalubale fa?
YAHAYA MAKAHO : Kalubalen farko da na fuskanta, lokacin da na ke neman yadda za a yi a san ni, in na yi waka na je ina so in kai wa mutum, ana kallo na a matsayin mai bara, in ina kokarin ganin mutum ba a bari na in gan shi, sai na yi ta fama, nai ta dawainiya. Na sha shan tafiyoyin kasa da dama. Na taba tafiya a kasa daga Rigasa zuwa NNPC. Na taba tafiya daga Funtuwa a kasa na ce ina neman Kaduna, duk da ban karaso ba. Na taka daga Kawo zuwa Rigasa ban san adadi ba. A lokacin in na rasa kudi, a kasa na ke tafiya. Akwai wata rana zan tsallaka titi, da ma na saba tsallaka babban titin Byepass ni kadai.
Ranar na tsallaka na farko, da na je na gaba na kasa tsallakawa, sai na yi ta tafiya a tsakiyar dakalin Babangida, sai na ji wata mata ta ce min za ka tsallaka ne? Sai na ce mata e, sai ta janyo hannu na ta maida ni hannun ta na hagu don ta rika ganin abin da ke zuwa ta daman ta. Sakin hannu na da ta yi ke da wahala, na dai ji karar gilas, ashe mota ce ta kwashe wannan matar aka yi wurgi da dan ta. A karshe wadanda su ka dauki matar su ne su ka tsallakar da ni. A duk lokacin da na tuna da wannan abin sai gaba na ya fadi. Ba zan iya mantawa da wannan abu ba!
FIM : Ko ka taba yin wakar da aka saka a fim?
YAHAYA MAKAHO: Ban taba yin wakar da aka saka a fim ba.
FIM : Amma ka na da sha’awa?
YAHAYA MAKAHO : A’a, ba ni da sha’awa.
FIM : Menene dalili?
YAHAYA MAKAHO : Dalili na, na farko mafi akasarin wakokin da aka fi so, su ne wakokin da su ka shafi soyayya. Duk da dai akwai mawakan da su ke yin waka ta soyayya, amma ta na dauke da wani sako na musamman. Akwai su da dama, kuma na san wakokin su. Ni ma in hakan ta kasance, zan yi wakar da ta shafi soyayya, amma mai cike da ma’ana, kuma zan so a saka ta a fim. Amma ba wakar da ake yi na gundarin kalaman soyayya ba.
FIM : A karshe, mecece shawarar ka ga mawaka ’yan’uwan ka?
YAHAYA MAKAHO : Har kullum dai abin da mu ka sani ne, duk abin da mu ka tsaya mu ka inganta shi, to zai zama mai inganci a wurin mutane. Abin da kuma ka yi shi da rashin inganci, zai zama ba shi da inganci a wurin mutane. Duk abin da ka yi ya zama sako, za a dade ana amfani da shi ko bayan babu ran ka. Duk kuma abin da ka saka son rai a cikin sa, ba zai zama abin alfahari ba. Sannan duk abin da za mu yi, sai mun sa hakuri a cikin sa.