Kannywood

Bidiyon rakashewa da ankayi wajen bikin “Birthday” din Fati Yola

Fitacciyar Jaruma a Masana’antar Kannywood Fatima isah Muhammad wacce akafi sani da Teemah yola ko kuma Rukayya acikin shiri me dogon zango labarina ta Shirya wani Kayataccen Shagali na bikin Ranar jagayowar Haihuwar ta.Bidiyon rakashewa da ankayi wajen bikin "Birthday" din Fati Yola

Jarumar ta jawo cece kuce tun bayan da aka hango yadda ta kayata wurin da akayi Shagalin Birthday din nata da yadda aka Zubar da Kudade masu yawo.

Mutane da dama sun bayyana ra’ayoyin su kan yadda Jarumar ta jijirce domin Shagalin yana daya daga cikin Shagalin Birthday dinda aka taba yi a Masana’antar Kannywood wanda yaja hankalin mutane duba da yadda akayi masa shiri na Musamman.

Jaruman Kannywood da dama sun samu damar halartar wannan Shagali irinsu Momee Gombe, Fatima Usman Kinal, Amal umar, Nana Izzarso da dai sauran su. Sun kuma tayata da Addu’a don ganin wasu Shekarun masu albarka.

Ga Vedion Yadda wurin ya kasance nan kamar haka.

 

[Via]Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button