Ni Ba Dan Siyasa Bane Kuma Ba Mawakin Siyasa Ba – Adam A Zango
Fitaccen jarumin fina-finan hausa kuma mawaki Adam A.Zango yayi kira cewa shi ba dan siyasa bane kuma baya wakan siyasa.
Jarumin wanda ke cikin fitattun jaruman masana’antar Kannywood dake goyon bayan zarcewar shugaba Muhammadu Buhari yace yana baiwa duk wanda yake so gudunmawa ta hanyar sana’ar sa.
Ya bayyana haka ne ta hanyar sako da ya wallafa a shafin sa na Instagram.
Ya rubuta “Ni ba dan siyasa bane kuma ba mawakin siyasa bane sai dai ina baiwa wanda nake so gudun mawa ta hanyar sana’a ta!! Bana cin tuwo da yan wawa.”
Ya kara da cewa “Duk wanda ya tsargu dashi nake yi,” tare da nuna alama cewa Buhari da El-rufai kadai zai mara wa baya a zaben 2019.
Ko a kwanan baya Zango ya jaddada cewa baya
baya siyasa don kudi kuma yana goyon bayan zarcewar Shugaba Muhammadu Buhari da gwamnan jihar Kaduna Mallam Nasir El-rufai domin sune zabin sa kuma zai cigaba da goyon bayan anniyar su gabanin zaben 2019.
Gwarzon jarumin yana cikin fitattun jaruman da uwargidan shugaban kasa Aisha Buhari ta karrama bayan kaddamar da sabuwar kudin makar yakin neman zaben Buhari mai taken “Sakamakon canji” a cikin watan Nuwamba