Ana kukan yunwa: Harajin da ƴan Nijeriya ke biya ya yi kadan – Bill Gates


Fitaccen Attajirin nan na duniya, Bill Gates wanda shi ne shugaban gidauniyar Bill da Melinda, ya ce harajin da ake karba a Nijeriya ya yi kadan.
Bill Gates ya yi bayanin hakan ne a taron tattaunawa na matasa kan samar da abinci mai gina jiki a Abuja a jiya Talata.
Daily Trust ta rawaito cewa, Attajirin dan kasar Amurka yazo Nijeriya ne domin halartar taruka.
Da yake jawabi a taron, Bill Gates, ya ce karancin haraji da ake karba yana haifar da kalubalen kudi a fannin lafiya da ilimi.
Ya ce domin yan kasa su samu karfin gwiwa kan kokarin gwamnati na kula da lafiya dole ne a tabbata ana tafiyar da kudaden da ake warewa fannin lafiya a yadda ya dace.
Bill Gates ya ce, ” Tsawon lokaci akwai shirye shirye ga Nijeriya wajen samar da kudade ga gwamnati fiye da yadda ake a yanzu. Abinda Nijeriya ke karba na haraji ya matukar kadan”, inji shi
Daily Nigerian Hausa
![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)




![[Bidiyo] Ran Sheikh Bello Yabo Ya Ɓace Ya Roki Allah Yasa baiwa Yan Bindiga Dama su Kame su](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2022/07/maxresdefault.jpg?resize=390%2C220&ssl=1)

