Kannywood

Maganar Sadiq sani Sadiq yace bai da uban gida Ba Gaskiya ba ne – Bello Muhammad Bello

A kwanakin baya anyi fira da fitaccen jarumin masana’atar Kannywood Sadiq sani SadiQ wanda yanzu yake haskakawa a cikin shirin labarina mai dogon zango Alhaji Al’amin mainasara ankayi masa tambaya shin waye mai gidanka a masana’atar Kannywood?

SadiQ sani SadiQ ya furta cewa shi baida mai gida a kaf masana’atar Kannywood, wannan amsar ta baiwa mutane mamaki sosai ganin irin yadda tun a lokacin wasu ke cewa karya ne Ali Nuhu mai gidan sa ne, wasu suce Adam a zango mai gidanka ne.

Wasu kuma sune Bello Muhammad bello BMB mai gidanka ne.

A cikin hirar da jaruma Hadiza Gabon cikin Gabon’s Room show talk ta tambayi Bello Muhammad bello General BMB akan cewa tare kunka zo kannywood,kuma bai da uban gida?

Batun cewa Sadiq Sani Sadiq na cewa bashi da Uban gida wannan ba Gaskiya bane domin nine na fara sakashi a film nine na kaishi wajen Ali Nuhu, nasan Sadiq a Jos Irin Yaran Unguwa ne ‘yan Daba domin baya ji ko a lokacin da na sanshi nine Uban gidan sa Amma Kasan Dan Adam a lokacin da Nasara tazo Masa Yana iya Mantawa -inji Bello Mohammed Bello BMB.

Saurari cikakken yadda haduwar da SadiQ sani SadiQ a cikin wannan bidiyo.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button