Kannywood

Wadanda suka sace ni sunce suna nan suna farautar Shugaba Buhari da Atiku Abubakar – Salisu Mu’azu

Salisu Mu’azu Jos darakta ne na masana’antar fina-finan Hausa na Kannywood, sannan kuma shine mataimakin shugaban masana’antar na kasa

– Kwanan nan aka sace, shi da wasu mutane biyu, kusa da kauyen Jingir dake karamar hukumar Bassa, jihar Filato, a lokacin da suke kan hanyar su ta komawa garin Jos daga Kaduna

A wata hira da yayi da manema labarai ya bayyana irin halin da ya shiga lokacin da yake hannun barayin.

Dan Jarida: Zaka iya tuna abubuwan da suka faru a ranar da aka sace ka?

Salisu Mu’azu: Ni da yayana, Sani Mu’azu Jos, da Danlami Yanke-Yanke da kuma Andy Bature, mun halarci wani taro da babban bankin Najeriya ya hada akan kananan masana’antu a Kaduna. Bayan an kammala taron, mun bar garin Kaduna zamu je Jos da misalin karfe 4 na yamma. Mun tsaya a Saminaka mun sha ruwa, muka cigaba da tafiyar mu, sai da muka je wani daji kusa da kauyen Jingir kawai sai muka ji harbin bindiga, sai wasu mutane suka fito mana suka ce mu tsaya. Muka tsaya, sai suka fito damu suka fara dukan mu. Sai nake gaya musu su daina dukan dan uwana saboda bashi da lafiya, sai suka kyaleshi. Sannan suka bashi wayarshi, suka tambayeshi ko zai iya tuka mota yace eh, sai suka kyaleshi ya wuce.

Wadanda suka sace ni sunce suna nan suna farautar Shugaba Buhari da Atiku Abubakar – Salisu Mu’azu
Dan Jarida: Barayin guda nawa ka gani a lokacin?

Salisu Mu’azu: A lokacin hankalina baya jikina, amma da na fara dawowa hayyacina na kirga kusan guda takwas, dukkan su basu wuce shekaru 20 ba zuwa kasa, kuma dukkan su Fulani ne.

Dan Jarida: Menene ya faru kuma bayan sun bar yayanka ya wuce?

Salisu Mu’azu: Bayan sun barshi ya wuce, sai suka ja mu cikin wani daji, inda muka yi tafiya a kafa ta kusan awa shida, sannan suka barmu muka huta. Ba a wani jima ba suka tambayeni wa zasu kira ya kawo kudin fansa. Sannan kuma suka tambayeni nawa zan iya bayarwa, sai nace musu miliyan daya, kawai sai suka hau ni da duka.

Bayan sun gama dukana, sai muka cigaba da tafiya, inda muka kai gurin wani tsauni, muka hau kanshi, sai muka iso bakin wani dutse mai kogo, sai suka daure mu a bakin dutsen na tsawon kwana uku, ruwan sama da rana duka ya kare a kanmu.

Babu zancen abinci fa. Idan suka lura cewa mun galabaita sai su bamu mangwaro da ruwan sama mu sha.

Dan Jarida: Banda ku kaga wasu mutane da suka kama a gurin?

Salisu Mu’azu: Mun ga mutum daya kawai a gurin a daure. Daga baya sun harbe shi ya mutu, bayan sun tambayeshi nawa zai iya biya yayi shiru.

Na ji tsoro mutuka, saboda suna yi mana barazanar cewa zasu kashe mu. Ba su saka mu ko kadan a hirarsu. Amma daga baya da muka cigaba da magana akan kudin fansa, sun fara saukowa, inda suka fara sanya mu a cikin maganganunsu kadan-kadan. Suna yawan kiran Yanke-Yanke, wanda daman shi yana da barkwanci. Ya na yawan saka su dariya, daga baya dai mun saba dasu sosai.

Daya daga cikinsu ya fada min cewa zai daina satar mutane idan ya samu naira miliyan dari, ko kuma idan ya samu nasara gurin sace shugaban kasa Muhammadu Buhari ko kuma tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar. Na yi dariya sosai da jin maganar shin nan.

Dan Jarida: An samu sabani akan kudin da ka biya na fansa, wasu sunce miliyan 10 wasu kuma sunce miliyan 3.5, ko zaka iya fada mana gaskiyar nawa ne ka biya?

Salisu Mu’azu: Da farko sun nemi na basu miliyan 10 ne. Amma daga baya bayan sun fuskanci cewa bamu da wannan kudin, sai muka fara ciniki. A karshe dai sun yarda akan cewa zasu karbi naira miliyan 3.5.

®L

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button