Labarai

Kaddara ko Ganganci : Matashin da ya hallaka budurwa a otel din Ifoma a Sokoto ta mutu



 

An cafke matashin da ake zargi da kashe budurwa a otal din ifoma da ke jihar Sokoto inda yayi amfani da wuƙa ya cakawa yarinya har ta mutu.

Manema labarai sun zanta da matashin mai suna Saifullahi hassan inda yake cewa.

“Kaddara ce da jarabawa da sherin shedan dan nima ba’a so na bane, saboda mun samu saɓani ne da ita akan wasu maganganu har ta kai da tana zagina shine kawai abin da ya faru.

Sai na sanya mata wuka da naji zata tonamin asiri, saboda muna tare da ita nasan ta -inji Saifullahi.

Saifullahi yace duk kaddara da ta samu mutum ana so yayi imani da ita kuma na yarda na aminta ina neman sasauci a taimaka.

“Ina kira da masu aikata laifi irin nawa da su ji tsoron Allah su daina , saboda wannan duniyar ba mata ba ta bace za’a koma ga Allah , nima dana aikata wannan abun nayi nadama.

Nan take samun rahoton samuwar wannan aika aika Kwamishinan lamuran addini a jihar Sokoto Dr. Jabir sani maihula ya rufe wannan otal din domin kada a cigaba da aikata irin Wannan mummunan abun a garin Sokoto.

 









Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button