Take-Taken Tinubu Sun Nuna Bai Damu da Gyara Tsaron Arewa Ba – manyan arewa


Kungiyar dattawan Arewa ta caccaki shugaban kasa Bola Tinubu kan mayar da hankali a lamuran tattalin arziki maimakon tsaro a kasar
Farfesa Usman Yusuf, jigo a kungiyar NEF, ya ce ya zama wajibi Shugaba Tinubu ya kafa kwamiti don bincike kan harin da aka kai jihar Kaduna
Kungiyar ta kuma gargadi shugaban kasar da ya tsame hannun jami’an soji daga wannan bincike, ya bar hukumomin fararen hula su yi
Kungiyar dattawan Arewa (NEF) ta ce take-taken Shugaba Bola Tinubu tun daga kalamai da abubuwan da yake yi sun nuna karara bai damu da matsalolin tsaron Arewa ba.
Farfesa Usman Yusuf, ya bayyana hakan a wata tattaunawa da gidan talabijin na Arise a ranar Talata. Dattawan Arewa sun ce shugaban kasa Tinubu bai damu da matsalar tsaro a Arewa ba, ya fi mayar da hankali kan tattalin arziki.
A cewar sa, babu abin da shugaban kasar ya mayar da hankali kan sa sama da tattalin arziki, duk inda kudi za su shigo, to can ne za a ga mutanensa,
Vanguard ta ruwaito.
“Amma duk abin da ya shafi tsaro, ‘kamar su yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauransu, ba ta su yake yi ba, don ba su ne a gabansa ba. “Babu mai tsawatarwa jami’an soji yanzu, duk abinda suka ga dama shi suke yi.
Yanzu gashi sun fara sakin bam a kan jama’armu, kuma ba wanda ya isa ya kalubalance su.” A cewar Farfesa Yusuf. Ya kuma yi nuni da cewa ko a kasar Amurka da Najeriya ke kwaikwayon shugabancin ta, hukumomin farar hula ne ke sa ido kan ayyukan rundunar sojin kasar.
Ya kalubalanci aikin da ya rataya a wuyan ministan tsaro, inda ya yi ikirarin cewa shugaban kasar ya damka lamuran tsaron kasar hannun dakarun soji. Ya kuma yi kira da a gaggauta yin kwakkwaran bincike kan harin da aka kai wa masu maulidi a jihar Kaduna, inda ya ce jami’an soji ba za su yi adalci wajen bincikar junansu ba.
Jigon kungiyar dattawan Arewan, ya kuma ce: “Duk abin da shugaban kasar ke shirin yi, to ya sani cewa ba mu yarda jami’an soji su binciki kansu ba.
Mun ga ire-iren wadannan misalan, kuma babu wani sakamako mai kyau da aka samu. “Dole a samar da wani kwamiti da zai yi binciken karkashin tsohon babban joji na kasa, tsaffin hafsoshin tsaro, masu sarautun gargajiya da malaman addini, wadanda suka damu da rayukan al’umma.”