Kwaɗayi ya cinye matasa ba su da tasiri a siyasar Najeriya


Wani tsohon minista a gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo ta 1999, ya soki matasan Najeriya saboda gazawarsu wajen tashi su ƙwatarwa kansu ƙwaƙƙwaran gurbi a harkokin siyasar ƙasar.
Alhaji Sani Zangon Daura ya ce ba a ga wani tasirin matasa a harkokin siyasar ƙasar ba, saboda akasari matasan sun zama masu kwaɗayi da rashin alƙibla, abin da ya sa wasu ke amfani da su kawai a matsayin karnukan farauta.
“Yanzu ba ka da wata jam’iyya ta samari. Duk wanda (ka ga) ya fito, kuɗi yake nema.”
A cewar tsohon ministan noman zamanin gwamnatin Obasanjo, kamata ya yi matasa su kasance a kan gaba wajen kawo sauyi da ƙwatowa al’umma haƙƙi, amma ba haka lamarin yake ba a yanzu.
Ya bayyana damuwar cewa matasa sun zama lusarai ta yadda har “suna gani ana cutar su, ba sa iya komai”.
Sani Zangon Daura na wannan jawabi a wani ɓangare na hirarrakin da BBC ta yi da ƙusoshin ‘yan siyasa a kan cikar mulkin dimokraɗiyyar shekara 25 a Najeriya.
Ya dai ce a ganinsa, dimokraɗiyyar Najeriya ba ta samu wani ci gaban a-zo-a-gani ba, saboda har yanzu talaka ba shi da ƴancin zaɓar shugabannin da yake so su jagorance su.
Murya ‘yanci
Join Our WhatsApp Channel
Get verified job vacancies, career tips, scholarships and opportunities delivered straight to your phone, free and as soon as they're posted.


![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





