IMF ta Damu kan yadda Tinubu ya dawo da tallafin mai a boye -Ta Jero Matsaloli
Yayin da ‘yan Najeriya ke kokawa kan cire tallafin mai, hukumar IMF ta nuna damuwa kan halin da ake ciki Hukumar ta ce yadda Bola Tinubu ya dawo da tallafin mai a sirrance babu abin da zai tsinanawa kasar sai asara kawai
Ta bayyana cewa kasar za ta yi asarar fiye da rabin kudin shiga da ta ke tsammanin samu bayan dawo da tallafin a boye
Hukumar ba da lamuni da duniya (IMF) ta nuna damuwa kan yadda Bola Tinubu ya dawo da tallafin mai a boye. Hukumar ta ce dawo da tallafin da aka yi a boye zai cinye kusan rabin kudin shiga da kasar za ta samu daga arzikin man fetur.
Asarar da Najeriya za ta yi IMF ta ce matakin zai laƙume akalla N8.43trn daga cikin N17.7 trn da ake sa ran samu daga cire tallafin man fetur, cewar Punch.
Wannan na kunshe ne a cikin wani sabon rahoto da hukumar ta fitar kan Najeriya game da tallafin man fetur, cewar Leadership.
IMF ta ce taso a shafe maganar tallafin mai gaba daya a Najeriya cikin shekaru biyu kacal yayin da gwamnati ke kokarin kawo wasu shirye-shirye. Najeriya ta na shigo da gas kasar Sai dai duk da yawan fitar da mai da Najeriya ke yi, ta na shigo da mafi yawan gas kasar saboda ba ta da matattun mai da za su wadaci ‘yan ƙasar A wani bangaren, Bankin Amurka ya ce Najeriya za ta rasa N7bn zuwa N10bn idan ta bukaci shigo da litar 18 zuwa 25 na gas.
Wannan martani na hukumar na zuwa ne kusan shekara guda bayan Tinubu ya sanar da janye tallafin mai a kasar. Shugaban ya sanar da hakan ne a ranar 29 ga watan Mayun 2023 yayin kama rantsuwar mulki a birnin Abuja. “Tallafi ba zai ci gaba da samar da abin da ake nema ba yayin da tattalin arziki ke sake durkushewa.”
Dalilin cire tallafi da Tinubu ya yi
Kun ji cewa Ministan yada labarai da wayar da kan jama’a, Mohammed Idrisya ce nan ba da dadewa ba ‘yan Najeriya za su fara ganin amfanin cire tallafin man fetur.
Idris ya ce Tinubu ya ɗauki matakin dakatar da biyan kuɗin tallafin man fetur ne domin amfanin kasar baki ɗaya.
– Muryar yanci