Kannywood

Duk macen da ke da niyyar shiga harkar wasan Hausa ta dakata kada ta shigo – Alhassan Kwalle

Shugaban ƙungiyar jarumai ta masana’antar Hausa ta Kannywood Alhassan Kwallai, ya ce duk macen da ke da niyyar shiga harkar wasan Hausa ta dakata kada ta shigo.

Alhassan Kwallai, ya bayyana hakan ne yayin zantwarsa da Dala FM Kano a yau Alhamis, ya ce kasancewar suma jaruman matan na Kannywood sun yi musu yawa, a dan haka ne yake shawartar su da su haƙura da shigowa harkar Film ɗin, domin nan gaba kaɗan ma za su rufe ƙofar shiga saboda a cikin masana’antar babu abinda babu sai rashin tsari.

A cewar sa, “Dalilin jarumai Mata yaje kotu a lokuta da dama domin a warware matsalar su, a dan haka ne ma nake shawartar su da su zauna a gidajen su ko kuma yin aure, saboda ba sai sun zo masana’antar Kannywood sannan za suyi kuɗi ba, “in ji Kwallai”.

Ya kuma ƙara da cewa dangane da dambarwar da ke faruwa a kan jarumin masana’antar Adam A Zango, ba shi da ta cewa, domin mutum yana magana ne aka abinda ya sani, shi kuwa bai san komai ba akan abinda ya shafi Zangon.

Wakilinmu Abubakar Sabo ya rawaito cewa Alhassan Kwallai, ya kuma ce babu wata shawara da zai bai wa ƴan masana’antar domin kuwa mutuwa ma ta ishi kowannen su wa’azi, irin su rasuwar Jaruma Saratu Gidaɗo Daso, da ta Aminu S Bono, da sauran al’umma, kada Allah yasa ma su gyara halin nasu ga su ga Allah nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button