Kannywood

Adam A zango yayiwa Tijjani Asasse martani mai zafi

Fitaccen jarumi tijjani Asasse yayiwa adam a zango martani akan cewa wasu sun butulci ce masa wanda duniya kannywood ta girgiza wanda mun kawo muku bayyanin tijjani Asasse na kusan minti goma.

Adam a zango shima yayiwa tijjani Asasse martani a cikin wani faifan bidiyo inda yake bi daki daki yana mayar masa da martani akan jawabansa.

Ga abinda adam a zango ke cewa.

“Gaskiya ne kun nunamin soyayya sosai , amma nima na so ku, kuma na rantse da darajar ma’iki soyayar da nayi muku bakuyimin irinta ba, kuma ina so tijjani karka manta a wannan lokaci ku na miƙawa rayuwata saboda shekaru a lokacin ba su da yawa, rayuwata a hannun ku take domin duk abinda kunka gani kunka gayamin na yarda, duk abinda kun ka jiyo kunka gayamin na yarda.

Duk wanda kunka nunamin wannan masoyina ne na yarda, duk wanda kunka nunamin kun kace makiyina ne na yarda, to kenan idan har nayi wasu kura kurai a lokacin kune sila, domin duk wanda yake a masana’atar Kannywood yasan da wannan lokacin saboda haka babu karya a wannan bangaren.

Baba na bai taba son wani mutum a jarumai kamar adamu ba, haka mahaifiyata amma adamu bai yimin zo min ta’aziyya su ba – Tijjani Asasse

“Iyayen ka Allah yayi musu rasuwa ban zo nayi maka ta’aziyya ba, sai dai a lokacin ka manta ina da matsala da gwamnatin kano ina samame na, saboda a lokacin idan anka zo bikin sallah ina bisa kan wasa sai na hau wakar adam zango mai gari , sai nace inna ga dama gidan kwankwaso zan kwana, inna ga dama gidan Abba zan kwana, inna ga dama gidan sarki zan kwana lokacin sarki sanusi.

Sai anka kirani anka ce wannan abu da kake fada za’a kama ka, wannan dalili yasa na dauke kafa zuwa kano, na kira ka a waya nayi maka ta’aziyya , nayi fustin namaka ta’aziyya saboda wannan shine kadai abinda zan iya yi a lokacin.

Daga baya nazo na fara shiga kano kuma karka manta a lokacin da kayi gobara har gidanka naje kuma har gudumuwa na dauka na baka saboda ina da ikon a lokacin.

Kun samu matsala da sanusi wanda kuna yin aikin a duniya ne matsala dai ban san inda abun ya faru ba, abinda Sanusi ya gayamin da wanda ka gayamin ko wane da bambamci na dauki kafa naje har ofis dinka domin ana cemin kana zagina ban yarda ba.

Akwai manya manyan maganganu da ya dace ku saurara da kunnen ku ji yadda ta kaya a cikin wannan faifain bidiyo.

Ga bidyon nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button