Kannywood

Tijjani Asasse Ya Ragargaji Adam A. Zango Kan Jifar Su Da Yi Masa Butulci

Fitaccen jarumi Tijjani asase yayi wani bidiyo akan adam a zango da yayi akan yana cewa ya taimawa wasu mawaka da jarumai ya taimake su amma sunyi mishi butulci.

A cikin bidiyon yake mai cewa.

“Hakikanin gaskiya akwai wadanda adam a zango ya baiwa mota ya lissafa sunan su ya baiwa wane kaza yayiwa wane kaza a midiya da baiyi ba, kuma baya dauka hoto idan ya bayar , da wanda ya dauka ya bayar ya dauki hoto da adam a zango yanzu tafiya duk ta zama daya.

Minene na dauka hoto fada a midiya to shi kuma yanzu fa, fada ne a midiya duk ya zama daya.

Anyi anyi kar nayi magana akan adamu amma zuciyata ta gaza hakuri amma ba zan fadi sharri akan sa ba,kuma bazan fadi kura kuransa ba amma zan fadi wasu abubuwa yadda mutane zasu fahimta suyi muna adalci, kawai adalci da nake da mutane suyi mana.

Hakiƙanin gaskiya bamu taɓa son mutum a masana’atar fim kamar adamu ba, kuma zan iya fada ko shi ya sani a gaban kowa zan fadi, akwai wasu jarumai guda biyu a masana’atar fim Ali nuhu, adam a zango.

Ali Nuhu duk wanda yake karkashin sa ya damu da shi, shima ya damu da shi, babanka zai mutu zai jema gaisuwa ,babarka zata mutu zai jema gaisuwa, baka da lafiya zai kira ka ya tambaye ka lafiyar ka, idan zakayi fim ali nuhu zai maka sim, zai maka role ya taimakeka a wurin aikinsa.

Idan ka kira wayarsa zai saurare ka ko kai waye har ya zolaye ka baka kirasa ba Ali nuhu-inji Tijjani Asase

Shi kuma kanensa Adam A zango balalle ka kirasa ya ɗaga wayarka ba,balalle babanka ya mutu ya jema gaisuwa ba, balalle babarka ta mutu ya jema gaisuwa ba, amma shi ana arziki da shi.

Lokacin da nasan adamu, akwai lokacin da aka kirasa akace yana hassada na karyata saboda shi abokin arziki ne, ba abokin hassada bane, ba mahassadi bane, amma da anka fadamin ban yadda ba arziki akeyi da shi.

Adamu yana da kayan aikin fim

Adamu yana da light yana da Camera yana da gidansa yana da waye yana da kayan aikinsa azo ayi fim kudin abinci ayi talla a tallatashi a dauka a baiwa falalu yaje ya sayar idan an samu naira miliyan biyu kwandala bazai dauka ba ya dawo maka da kudin ka, kaima ka samu jari kaima ka zama mutum , ka gane cewa shi arziki ake yi da shi,amma kuskuren sa da shi , da ya ALLAH ta da kansa.

Akwai tarin manya manyan maganganu da zaku saurara a cikin faifain bidiyo nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button