Addini

Saɓawa Allah ne salwantar da rayuka da tayar da hankalin al’umma – Dr. Abdallah G/kaya

Advertisment

Limamin masallacin juma’a na Usman Bin Affan dake unguwar Gadan Kaya Dakta Abdallah Usman Umar, ya shawarci al’umma musamman ma matasa, da su kaucewa barin yin amfani da su wajen tayar da hankalin al’umma, domin kuwa hakan ya sabawa addinin musulunci.

Dakta Abdallah Gadan Kaya ya bayyana hakan ne ta cikin shirin Rayuwa abar koyi na nan gidan rediyon Dala FM, da ya gudana da safiyar juma’ar nan, ya kuma gargadi al’umma da su kaucewa sanya kansu cikin rikicin siyasa da har take kaiwa a wasu lokutan da zubar da jinin al’umma wanda hakan laifi ne babba.

Kashe-kashe da kone-kone ba abinda yake haifarwa face koma baya ga zaman lafiya da kuma durkushewar taltalin arziki da sauran bangarori a Kasa, “in ji Dr. Abdallah”.

Wannan dai na zuwa ne a dai-dai lokacin da al’umma ke dakon hukuncin da kotun kolin kasar nan zata yanke na gwamnan Kano a juma’ar nan 12 ga watan Janairun 2024.

~Dala fm

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button