MashaAllah Alhamdulillah! Yanda A Gudanar Da Daurin Auren Babban Malamin Nan Shiehk Aminu Ibrahim Daurawa Da Amaryarsa Hafiza Haulat Aminu Ishaq, A Yau Jumma’a Ne Dai Dai Da 21/10/2022 Aka Daura Auren Babban Malamin.
Malamai Da Dama Ne Su Halarci Daurin Auren Malam Aminu Ibrahim Daurawan. Inda Zuwa Yanzun Malamin Ya Angonce, Muna Fatan Ubangiji Allah Ya Basu Zaman Lafiya Da Kwanciyar Hankali Da Kuma Zuriya Dayyiba Amin Summa Amin.
A jiya shehunan malamai sun halarci daurin auren ash sheikh Aminu Ibrahim Daurawa tare da amaryasa hafiza Haulat Aminu ishaq wanda mu iya ce muku yawan malamai da Almajirai da sunka halarci wannan daurin aure suna da yawan gaske.
Duk a cikin wannan bidiyo zaku gansu wanda nan take bayan daurin auren anka fara walima da nasiha kamar yadda malamai ahlus sunnah sunka saba yi wanda abun burgewa harda ango yana cikin malamai da suyi karatu a walimarsa Allahu Akbar.
A madadin CEO hausaloaded tare da mabiya wannan shafin muna yiwa wadandan amare fata nagari Allah ya bada zuri’a dayyiba yasa duk hafizan Alkur’ani mai girma ne tare da karantarwa irin ta mahaifinsu.