Addini

Mu Yiwa Kan Mu Hisabi Kafin a Yi mana Tambayoyi (50) ~ Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa

 Muna cikin wani zamani, da mutane, sunfi damuwa da bayani akan wasu fiye da kansu, sunfi binciko laifin wasu fiye da nasu, Sayyadina Umar Yace kuyi kanku hisabi kafin ayi muku, Abubawan da suke jawo tsira, Bautawa Allah shi kadai da iklasi, akan sunnar Manzon Allah, a cikin Akida, da Ibada, Da mu’amalah, da Halaye masu kyau, yi kanka tambaya, hamsin don kasan matsayinka :
Allah yasa mu dace :
1- waye ya yika ?
2- mai yasa ya yika ?
3- kai waye ?
4- A ina kake ?
5- mai kake yi ?
6- Ina zaka ?
7- mai zai faru ?
8- Abinda kafi so a rayuwar ka yayi daidai da abinda Allah yake so?
9- Abinda kafi ƙi a rayuwar ka yayi daidai da abin da Allah yake ƘI?
10- Duk abinda kakeyi, kana tambaya kafin kayi?
11- su waye abokanka?
12- Yaya zamanka da iyayanka?
13- Yaya zamanka yake da iyalanka?
14- Wace kungiya kakeyi don me?
15- A kwai wani yanzu haka da bakwa shiri da shi?
16- Tsakaninka da Allah ka taba cin amanar wani?
17 Kanayin karya?
18- Kana Dun guma ashariya?
19- Yaya zamanaka da makotanka?
20- Wace shedar ilmi kake dauke da ita?
21- kana salloli a Jam’i musamman a masallaci?
22- yaya alakar ka da danginka take ?
23- shin kana sada zumunta?
24- shin kana bayar da sadaka ?
25- shin kana karanta Alkur’ani mai girma kullum ?
26- kana azumin litinin da Alhamis?
27- kana sallar Shafi’i da wuturi?
28- kana zuwa asibiti domin ziyarar marasa lafiya?
29- Kana yawan saba alkawari ?
30shin kana azumtar kwanaki masu haske, ranar sha uku, sha hudu, sha biyar?
31- shin kana kiyamul- laili?
32-kana umarni da kyakyawa da hani da mummuna?
33-  kana zuwa aiki akan kari kuma ka tashi akan lokaci?
34- kana zuwa gaban malami domin daukar karatu?
35-ka tabbatar abinda kake ci  halal ne?
36- kana kuwa damuwa da halin da yan uwanka musulmi suke ciki?
37- kana taimaka marayu kuwa?
38- salati nawa kake yiwa Annabi saw kullum?
39- Istigfari nawa kakeyi kullum?
40- kana zuwa makabarta domin tuna lahira?
41- kana zuwa taaziyya da sallar Jana’iza?
42- Shin kana zikrin safe da yamma ?
43- shin kana yiwa dukkan musulmi sallama ko kuwa sai wanda ka sani?
44- kanayin rantsuwa akan karya kuwa?
45- kana shan taba ko wiwi ko giya ko hodar iblis?
46-  kana jin kade- kade, da wake- wake na batsa ?
47-  kana Canja halittar ka?
48- ka taba karbar cin hanci?
49- kana kyautawa iyalanka?
50-  kana gaba da wani kuwa? Idan kana gaba dashi da wane dalili?
Mu duba maga maki nawa muka samu a cikin jerin waɗannan tambayoyi?

Idan muna nanatawa kammu waɗannan tambayoyi kuma muna ƙoƙarin nemo amsa, zai sa mu ragewa kan mu , hisabi, wajan gyara abinda muna ɓata kafin lokaci ya ƙure da kuma ƙara  aikin alheri, domin makomar mu
Maimakon surutu mai yawa mara amfani da muka cika shafukan mu da su.
Allah ya agaje mu.

Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button