Hikimomin Yin Aure – Sheikh Aminu Ibrahim Daurawa
Na ɗaya a addinance,
1.Yin biyayya ga umarnin Allah, wanda acikin haka akwai rabon duniya da lahira
2. Biyayya ga Annabi saw, saboda aure ya tabbata a sunnar ta fuska uku, Annabi saw ya yi aure kuma ya yi umarni a yi aure, kuma ya tarar ana aure ya tabbatar tare da yin wasu gyare gyare.
4. Acikin yin aure akwai toshe kafar sheɗan, ta kallon abin da ya haramta ko wajan faɗawa zina ko maɗigo, ko liwaɗi ko neman dabba, ko amfani da hannu, ko sauran hanyoyi na sheɗanci.
5. Acikin aure akwai biyan sha’awa ga ma’aurata da kuma samun lada.
6. Acikin akwai rage yawan ƴanmata da zawarawa, a cikin al’umma, wanda yawan su tare da samari ba tare da aure ba, ya na barazana gamai da ɓarkewar annoba, ta zinace – zinace, haka kuma yana kawo cututtuka da saukar fushin Allah, wanda ya hana kusantar zina.
7. Acikin yin aure akwai samun zuriya, wacce za a yi mata tarbiyya mai kyau a gaban uwa da uba da renan al’umma ta gari.
8. Acikin aure akwai samun nutsuwa da kwanciyar hankali, da Soyayya tsakanin miji da mata.
Manzon Allah saw yace babu abinda ya dace da masoya irin su yi aure.
9. A cikin yin aure akwai samun lada mai yawa wajan ciyar da iyali da ɗaukar nauyin su da sauran hidmomin su na yau da kullum, duka yana shiga cikin sikelin lada na mutum a ranar alƙiyama
10. A cikin aure zaka samu jari na ɗa ko ƴa ta gari wacce za su dinga yi maka addu’a ko bayan mutuwar ka bar sadaƙa jariya,
11. A cikin aure akwai idan ka haifi ƴaƴa suka mutum suna ƙanana, za ka amfana da su ranar alƙiyama, kamar yadda ya tabbata a hadisi
12. Idan mutum ya yi aure sai Allah ya bashi ƴaƴa mata daga biyu zuwa sama, ya tsaya ya kula da tarbiyyar su da dukkan buƙatun su na ilmi da tarbiyya da lafiya da sutura har suka girma ya yi musu aure, Aljanna ta tabbata a gare shi. Kamar yadda ya tabbata a hadisi.
13. Aure yana kare addini, wanda ya yi aure ya cika rabin addininsa, ya ji tsoran Allah shine cikon rabin. (Hadith).
14. Aure yana kare rayuka da rayuwa ya na hana yaɗuwar cutaka masu kisa kamar HIV,
Aure yan kare mutunci, anfi ganin mutuncin masu aure ko da kuma marasa auran suna da mutunci.
15. Aure yana ƙara kaifin hankali domin da yawa marasa aure suna samin ciwon hauka saboda zaman kaɗaici da takaici da rashin abokin zama yake haifarwa.
Aure yan ƙara yawan dukiya domin mafi yawan masu arziƙi suna da aure.
16. yin aure yana tsare yawan shan magunguna na ƙarya sha’awa wanda hakan yana barazana ga lafiyar maniyyi da ƙarfin ɗa namiji
17. Aure yana rage wahalar siyan abinci.saboda kana da mai dafa maka abinci a gida.
Aure ya na tsare yaɗuwar Fyaɗe, a cikin al’umma da ƴaƴan shegu, duk da ba laifin su bane.
18. A cikin littafin ihya’u ulumidden. 2/72 na Al’imam Garzali, ya kawo ƙissar wani bawan Allah, wanda ake bashi shawara ya yi aure tun da yana da halin riƙe matar sai yaƙi yi. Bayan ɗan wani lokaci sai ya kwanta bacci, yana tsakar bacci sai a ka ga ya tashi a firgice ya na cewa, don Allah ku aurar da ni, sai aka ce masa mai ya faru? Sai yace :na yi mafarki a cikin wannan baccin alƙiyama ta tashi, muna tsaye cikin damuwa da baƙin ciki ga ƙishrwa mai tsanani muna ciki haka sai ga wasu yara suna ɗauke da wasu fitilu masu haske da kofuna a hannun su na zinarai da azurfa suna shiga cikin mutane suna bawa wasu daga ciki ruwa suna tsallake wasu sai nace ku taimake ni da ruwa ina jin ƙishrwa mai tsanani, sai suka ce ai baka da ɗa a wannan wajan mu muna shayar da iyayan mu ne waɗanda suka haifemu, muka mutu kafin su.
yace wannan shine dalilin da yasa nace kuyi mini aure ko Allah ya azurtani da ɗa na gari da yi mini addu’a idan na mutu idan kuma ya riga ni mutuwa ya taimaka ni a wannan wajen.