Labarai

Da mijina ya sadu da ni gara ya rika wasa da al’aurar sa har ya yi inzali – wata Mata a Kotu

Advertisment

Wata matar aure kuma ‘yar kasuwa mai suna Doris Unekwu a ranar Alhamis ta roki kotu a Jikwoyi, Abuja da ta raba auren ta da mijinta Matthias saboda rashin saduwa da ita da ba ya yi.

Doris ta ce mijin ta Mathias yakan killace kansa yayi ta wasa da al’aurar sa har sai yayi Inzali maimakon ya zo gareta su sadu.

Premium Times hausa na ruwaito cewa ,Doris ta ce Matthias na yawan cin zarafin ta ta hanyar yi mata dukan tsiya da zaginta a duk lokacin da ta bata masa rai.

“Babu abin da ban yi ba domin jawo hankalin mijinta amma duk a banza. Wata rana na kama shi yana wasa da al’aurar sa sannan ya bayyana mun cewa yana haka ne domin koyan wani abu da ya gani a yanar gizo.

“Wata rana kiri-kiri Matthias ya ce mun ya gwamnace ya bata lokacin sa yana hira a waje da ya dawo cikin gida domin wajen ya fi masa kwanciyar hankali.

Doris ta ce a dalilin haka ya sa ta hakura da zaman auren Matthias.

Shi kuwa Matthias ya musanta duk abin da Doris ta fada a kansa.

Alkalin kotun Thelma Baba ta shawarci ma’auratan da su je su sassanta kansu a gida.

Thelma ta ce za a ci gaba da shari’ar ranar 31 ga Janairu.

Wani labari daban : Farashin Kayan Abinci A Kasuwar Batsari A Jihar Katsina

A yau Alhamis 19/01/2024. kamar kowane satin kasuwar garin Batsari ta ci cikin yardar Allah kuma mutane sun zo daga wuri daban-daban domin gudanar da kasuwanci kamar yadda aka saba a kowane satin duniya.

Kasuwar ta cika ta batse al’umma sun gudanar da kasuwancinsu cikin ƙwanciyar hankali saɓanin baya: ga wasu daga cikin farashin kayayyakin.

Kayan Abinci;
Buhun Masara 48000-49000
Buhun jar masara 51000
Buhun Shinkahwar Nigeria Babba 94000
Buhun jar dawa 41000
Buhun farar dawa 38000
Buhun farin Wake Kanana 68000
Buhun farin Wake Manya 70000
Buhun waken Suya 48000
Buhun Gero 44000
Buhun Gyada da aka bare mai 44 N88000

Kayan Cefane;
Buhun Tattasai Busasshe 65000-70000
Buhun Danyen Tattasai 21000-22000
Buhun Attaruhu 22000-23000
Solon Tattasai 11000-12000
Solon Attaruhu 13000-14000
Kwandon Tumatir 2000-2500-3000
Damen Albasa 2500-3000-3500

Sauran kayayyakin;
Buhun Rogo Mai Toliya 45000
Buhun Rogo Marar Toliya 41000-42000
Buhun Dankali Mai Toliya 17000-18000
Buhun Dankali Marar Toliya 13500-14000-15K

Buhun Barkono 38000-39000-40000
Buhun Goruba 4000 abunda yayi sama
Buhun Auduga duk kilo 450-460-470
Buhun Zobo yau ba’a auna gabana ba
Damen Rake 4000-5000-6000
Buhun Karas 6000
Buhun Yalo 4000

Allah Ya albarkaci wannan kasuwa ya ƙara bamu zaman lafiya a jihar Katsina da Najeriya.

Rahoto daga:
Comrd Abubakar Mu’awiya Batsari.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button