Labarai
Macen Farko Musulma Ta zama Mataimakiyar Sufeto Janar Na ‘Yan Sandan Nigeria
Advertisment
Daga Ibrahim Rabilu Tsafe
Hajiya Aisha Abubakar Baju daga jihar Adamawa ta zama mace ta farko musulma daga arewa da ta zama mataimakiyar Sufeto janar na ‘yan sandan Nijeriya wato AIG.
Kafin bata mukamin AIG ita ce Kwamishiyar ‘yan sanda mai kula da bangaren dawakai da dabbobi ‘yan sanda wato CP Veterinary.
AIG Aisha ta yi karatun boko har ta samu matsayin Ph.D, ta samu wannan karin girman shekaran jiya bayan zaman taro da hukumar kula da ‘yan sanda ta yi a jiya karkashin jagorancin tsohon sufetan ‘yan sandan Nijeriya IGP (Rtd) Musliu Smith.
Wanda Shafin rariya ne na wallafa labarin a shafinta
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





