Wannan zanba ce : bidiyon Miji Ya koka kan Yadda matarsa Take hana shi Jindadi In dare yayi ta rungume dan su
Wani magidanci ya garzaya soshiyal Midiya ya koka kan babbar matsalar da yake fama da ita game da mai ɗakinsa a gida.


Mutumin ya bayyana cewa matarsa ta maida hankali kacokan kan ɗan da suka haifa kuma ya wallafa bidiyon abokiyar rayuwar tasa tare da yaron na kwance a gado. Legit na ruwaito
Wanda ya wallafa bidiyon a TikTok ya rubuta cewa:
“Amma wasu matan da gangan suke wa mazajensu haka domin su baƙanta musu rai.”
An umarci Magidanci ya canza wurin kwanciya
Ya fara ɗaukar Bidiyon da nuna gadon wanda yaron ya maida wurin hutawarsa kana ya koka da halayyar matarsa na hana shi shigowa cikinsu a gadon aurensu.
Mutumin yace idan ta so zata maida yaron kan ɗan karamin gadonsa amma ta ƙi yin haka. Ya roki yaron ya tausaya masa ya koma kan gadonsa.
Matar, haifaffiyar ƙasar Ghana, an hangeta tana babbake sauran wurin da wani zai iya kwanciya a gadon da ɗayan hannunta don kar mijin ya hawo.
Kalli bidiyon anan
@bigmiller09 But some women intentionally do this for their husbands to feel bad #funny #learnontiktok #comedia #comment #duet #funnyvideos #viraltiktok #viralvideo #viral #new #newtrend #netflix #net #capcut #old #loveyou #lovestory #love #ghana #nigeria
Jama’a sun maida martani
Davilekimmy yace:
“Ai da zaran ka haihu, gaba ɗaya soyayyar da matarka ke nuna maka zata koma kan jaririn, daga miji zaka koma Bestie.”
Maggyhope yace:
“Ka jira har zuwa lokacin da matar zata haifi ɗiya mace, daga lokacim zaka gane danƙon alaƙar da take da yaron.”
Winnerbabywinner8 tace:
“Ka sha romon jin daɗi a lokacinka dan haka ka bar yaro shi ma ya mori na shi lokacin.”