Labarai

An daure wata mata mai shayarwa bisa laifin satar indomie

Babbar Kotun Tarayya da ke Ado Ekiti ta yanke hukuncin daurin shekaru hudu ga wata uwa mai shayarwa, mai suna Yinka Akinwande, bisa samun ta da laifin satar taliyar indomie da kuɗin ta ya kai kimanin Naira miliyan 5.5

A cewar bayanan tuhumar, wacce ake tuhumar “tsakanin watan Agustan 2015 zuwa Oktoba 2019 a sashin shari’a na Ado-Ekiti ta aikata laifin damfara ta hanyar karɓar kaya (indomie) daga hannun wani Bolanle Akarakiri .” Jaridar Daily Nigerian Hausa na ruwaito

An daure wata mata mai shayarwa bisa laifin satar indomie
An daure wata mata mai shayarwa bisa laifin satar indomie

Dan sanda mai shigar da kara, Samson Osobu, wanda ya ce wacce ake kara ta aikata laifin ne a lokacin da take wakiliyar tallace-tallacen mai karar, ta kira tare da gabatar da kayan a hannun shaidu guda biyu: wanda ya shigar da karar da kuma jami’in ‘yan sanda mai bincike, John Olotu.

Lauyan da ke kare mai wa ce a ke ƙara, R.A. Mohammed, ya roki kotun da ta yi wa wacce ake ƙara sassauci, inda ta ce wacce take karewa uwa ce mai shayarwa da jariri dan wata hudu.

Mai shari’a Babs Kuewumi ya ce ya yi la’akari da rokon jinkai da lauyan ya yi.

“Daga shaidar da mai gabatar da kara ya tabbatar, kotu ta samu wacce ake kara da laifi kamar yadda ake tuhumar ta. A nan na yanke wa wacce a ke tuhuma hukuncin zaman gidan yari na shekaru hudu,” in ji alƙalin.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button