Labarai
Gwamnatin Kano ta yi watsi da bukatar MDD kan wanda ya yi ɓatanci ga Annabi
Advertisment
Gwamnatin Kano ta ce ba za ta sauya matsayinta ko na kotun shari’a ba, kan hukuncin da aka yankewa yaron nan Omar Faruk kan laifin kalaman ɓatanci kan annabi, tare da cewa shekarun sa 16.
Asusun kula da ilimin kananan yara na Unicef ya bukaci gwamnatin tarayya ta taka rawa wajen ganin gwamnatin Kano ta gaggauta janye hukunci da sake nazarin shari’ar da ta yi wa yaron mai shekara 13.
A ranar 10 ga watan Agusta ne wata kotun shari’ar musulunci a jihar Kano ta yanke hukuncin shekara 10 kan yaron da aiki mai sassauci.
Bbchausa ta kara da cewa unicef a wata sanarwar da ta fitar a ranar Laraba a Abuja ta ce hukuncin ya ci karo da dokokinta na kare haƙƙin yara na 1991, da Najeriya ta aminta da shi.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com

![[Bidiyo] Ni na haɗa auren G-Fresh da Alpha Charles – Jaruma Babiana](https://i0.wp.com/hausaloaded.com/wp-content/uploads/2024/12/Picsart_24-12-25_12-05-31-313-scaled.jpg?resize=220%2C150&ssl=1)





