Labarai

Kotu ta ci tarar Gwamna Abba N25m game da shari’ar Alhassan Doguwa

Babbar Kotun Tarayya da ke zamanta a Abuja ta ci tarar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Naira miliyan 25 kan haddasa rudani da damuwa ga dan majalisar tarayya mai wakilta Kananan hukumomin Doguwa da Tudun Wada, Hon Alhassan Ado Doguwa.

Hakazalika, kotun ta kuma soke umurnin da gwamnan ya ba Atoni-Janar na jihar na sake duba shari’ar Alhassan Doguwa kan zargin kisa.

A zaman kotun na ranar Juma’a, Mai Shari’a Donatus Okorowo, ya umurci Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf, da kada ya sake taba ’yancin dan’Adam na mai kara Alhassan Ado Doguwa ko kuma tsoma baki a abin da ya shafe shi.

Wani labari : Jirgin sama mai saukar ungulu mallakin sojojin saman Nijeriya ya yi hatsari

Mai magana da yawun rundunar sojin saman Edwin Gabkwet da ya tabbatar da faruwar lamarin, ya ce babu wanda ya rasa ransa a yayin hatsarin, sai dai ‘yan raunuka.

Hatsarin ya faru ne a Fatakwal babban birnin jihar Rivers da sanyin safiyar Juma’a a yayin da sojojin ke kokarin kai samame wajen masu satar danyen mai.Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button