Labarai

Sanatoci Sun Yi Barazanar Karar Dangote da Kamfanoni 13 Zuwa Gaban EFCC kan N135bn

Matatar Dangote, Mob Integrated Services Ltd da gwamnatin Jihar Delta sun amfana da wani tallafin daga bankin CBN

Gwamnan babban banki ya raba N135bn a matsayin bashi ga masu harkar mai da gas, majalisa ta fara bincike a kan batun Agom Jarigbe ya ce za a dauki mataki bayan gano wasu sun karbi bashi amma ana zargin sun yi wasu abubuwa dabam

Sanatoci Sun Yi Barazanar Karar Dangote da Kamfanoni 13 Zuwa Gaban EFCC kan N135bn
Sanatoci Sun Yi Barazanar Karar Dangote da Kamfanoni 13 Zuwa Gaban EFCC kan N135bn

A ranar Alhamis, kwamitin majalisar dattawa, ya yi barazanar kai karar wasu kamfanonin mai da gas zuwa wajen hukumar EFCC. Premium Times ta ce kwamitin majalisar zai yi karar wadannan kamfanoni idan aka same su da laifin karkatar da tallafin N135bn da CBN ya bada.

Shugaban kwamitin harkar gas a majalisar dattawa, Sanata Agom Jarigbe ya aika da wannan gargadi sa’ilin da su ka yi zama da kamfanonin.

Sanatoci na binciken Dangote da kamfanonin mai a Majalisa

Bankin CBN ya fito da wani tsari inda ya tallafawa manyan kamfanoni da aron kudi, Sanatoci sun bukaci jin yadda aka yi amfani da bashin.

Su wani kamfanoni ne CBN ya ba bashi?

An rahoto Jarigbe ya na cewa NIPCO Gas Ltd ya karbi aron N25bn, NIPCO Plc (N5bn), Hyde Energy Ltd (N2bn), sai kuma Transit Gas Limited (N8bn). Akwai Lee Engineering & Construction (N15bn), Pinnacle Oil And Gas Fze (N10bn), kamfanin Amalgamated Oil (N5bn) da Gas Nexus Ltd (N10bn). Sauran wadanda su ka karbi aron kudin sun hada da matatar Dangote (N5bn), gwamnatin jhar Delta (N20bn), Novagas (N1bn) da Greenville (10bn).

Ina kamfanoni da gwamnati su ka kai kudin?

Sanatan na Kuros Ribas ta Arewa ya ce shi da ‘yan kwamitinsa a majalisar dattawa sun lura ba ayi amfani da bashin kamar yadda aka bukata ba.

Da aka tattauna da wakiliyar ma’aikatar harkar man fetur, Tribune ta ce Oluremi Komolafe ta nuna ba ta san CBN ta bada aron wadannan kudi ba. “Abin da kwamitin ya lura shi ne akwai haka-da-haka a lamarin kuma kwamitin nan ba zai fasa jawo EFCC su dawo da kudin ba.

Wasu da su ka ci moriyar tsarin ba su bi ka’ida ba. Alal misali, ma’aikatar harkar man fetur ba ta ma san an raba wadannan tallafi ba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button