Labarai

Kaico: Shekara Biyar Da Ritaya, Sufetan ’Yan Sanda Ya Koma Barace-Barace A Titi

Advertisment

Sauyin rayuwa ya sa wani Sunday Ogwo Okpalle, sufetan ‘yan sanda mai anini biyu da ya koma wa mabaraci a kan titunan jihar Niger.

Sunday Okpalle, ya shafe kusan rasuwarsa yana aikin dan sanda, matsayin mai bayar da hannu a kan titi a jihar.

Kaico: Shekara Biyar Da Ritaya, Sufetan ’Yan Sanda Ya Koma Barace-Barace A Titi
Kaico: Shekara Biyar Da Ritaya, Sufetan ’Yan Sanda Ya Koma Barace-Barace A Titi

A safiyar ranar Talata, wakilin jaridar Punch ya ci karo da Okpalle, wanda ke bin masu motoci, Keke Napep da ‘yan acaba yana rokon kudin da zai ci abinci.

“Ku taimake ni ko na sami na cin abinci,” ya ke nanata wa masu ababen hawan, wadanda ba sa ko kula shi.

Yayin da wasu suka ba shi taimako daga abin da suke da shi, wasu kuma sukan ce:

“Ku kyale shi, haka yake bara a nan kullum, ba ya ko gajiya.”

 

Takaitaccen bayani kan rayuwar Mr Okpalle

Da ya zanta da wakilin Punch, ya shaida masa cewa tsananin rayuwar da ya shiga ne ya tilasta shi yin bara, rashin yin hakan na iya saka shi kwana da yunwa.

Batu kan fansho da ya ke karba kuwa, ya tabbatar da cewa ana tura masa naira dubu talatin ne kuma kudin na zuwa ne a kurarren lokaci.

“Rayuwa ba ta yi mun kyau ba, shekara biyar da yin ritaya yanzu, ina da yara biyar da mata daya, amma sai na yi bara muke cin abinci.

“A lokacin da nake aiki, nakan samu naira dubu uku zuwa hudu kafin na tashi aikin ranar, amma yanzu ko sisi bana samu.”

Me ya faru da kudin giratutin Mr Okpalle?
A cewar Mr Okpalle, kamar yadda Legit ta ruwaito, inda ya kara da cewa:

“Sai da na yi shekara daya da rabi sannan na samu naira miliyan 1.7 na giratuti madadin miliyan 6. Haka na hakura, daga nan duk wata ake tura mun naira dubu talatin kudin fansho.

“Kudi sun zo sun kare saboda dawaniyar karatun yara da hidimar gida, karshe dai dole na dawo yin bara don ciyar da iyalina.”

A karshe ya roki gwamnatin tarayya da ta taimaka ta biya sa karashen kudin giratutinsa ko ya samu ya farfado daga wannan bakin talaucin da ya ke ciki.

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button