Labarai

Sojojin Sama Nijeriya sun ragargaje Yellow Yambros a kaduna

Jiragen sojojin saman Najeriya sun yi wa maboyar hatsabibin ɗan bindiga luguden bamabamai a Kaduna

Zaratan Sojojin Sama na Najeriya, sun kashe gogarman ɗan ta’adda, Yellow Jambros tare da rundunar sa, a hanyar Abuja zuwa Kaduna da kuma cikin Zamfara, Neja da Kaduna.

Haka nan kuma a lokacin an samu nasarar kashe ɗimbin dakarun sa a farmakin da aka kai masu dazukan Kaduna, Abuja, Neja, Katsina da Zamfara.

Rundunar Sojojin Najeriya ce bayyana haka, ta bakin Kakakin Yaɗa Labaran su, Edward Gwabkwet.

Ya ce an kashe Yellow Jambros da dandazon dakarun sa da suke ta’addanci da garkuwa da mutane, a lokacin da suke ƙoƙarin shiga wani ƙaramin jirgin ruwa domin su tsallaka Kogin Jikudna da ke Gundumar Kogo, a yankin Wurukuvhi, cikin Ƙaramar Hukumar Chikun, a Jihar Kaduna.

Gobkwet wanda Air Kwamanda ne, ya ce ‘yan bindigar sun yi tsammani sojoji sun dakatar da kai hare-hare ta sama, tun bayan babban kuskuren kai hari kan masu Maulidi, a Tungar Biri, cikin makon da ya gabata.

Gwabkwet ya ci gaba da cewa zaratan Sojojin Sama na “Air Components Operation Whirl Punch” ne suka kashe Yellow Jambros da dakarun ta’addancin sa.

Ya ce an kashe su Jambros a yankin Shiroro, cikin Jihar Neja, kamar yadda Kamfanin Dillancin Labarai na Najeriya, NAN ya ruwaito.

Sanarwar ta ce dakarun sojojin Najeriya sun bi sawun Yellow da abokan ta’addancin sa tun daga dajin Zamfara, har zuwa cikin dajin Neja, yayin da suke gudu kan babura 13 tsakanin kan iyakar Kaduna-Neja, yayin da suka nausa su ka doshi dajin Kasasu, a yankin Shiroro.

“A Kusasu, wasu ‘yan bindiga kan babura biyar sun bi zugar su Yellow Jamhros, inda babura suka kai 18 kenan, daga nan kuma suka doshi gaɓar mashigin Kogin Jikudna.

“A bakin mashigin Kogin Jikudna ne maɓarnatan suka hau wani kwale-kwale mai inji, tare da baburan 28, da nufin su tsallaka kogin don su haɗu da sauran ‘yan bindiga ‘yan uwan su da ke can tsallaken ruwa.

“Daga nan ne hukuma ta bayar da iznin a kai masu farmaki kawai.

“An samu nasarar kashe Yellow Jambros, dakarun sa, kuma an ragargaje baburan su da jirgin ruwan da suka shiga baki ɗaya.

Wani gogarman ɗan bindigar da aka kama a Zamfara cikin Oktoba, 2020, ya yi iƙirarin cewa a ƙarƙashin Yellow ya ke.

Ɗan ta’addar mai suna Mohammed Sani, ya kashe fiye da mutum 50 bayan ya yi garkuwa da su.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button