Labarai

Rashin fada mana gaskiya ne ya jefa Najeriya cikin rikici – Osinbajo

Advertisment

Mataimakin shugaban Najeriya, Yemi Osinbajo ya ce tashin hankalin da ake gani a kasar na faruwa ne saboda mayan kasar ba sa fitowa su fadawa gwamnati gaskiya.
Osinbajo ya fadi haka ne a wani taron tattaunawa na yan takarar APC da ke neman kujerar gwamnan Anambra wanda jam’iyyar APC reshen jihar ya shirya.
Bbchausa na ruwaito. Mataimakin shugaban kasar ya kuma ce Najeriya ba za ta so ta fada yakin basasa ba.
Osinbajo ya ce dole ne yan siyasa su kara himma wajen fadin gaskiya da kuma daukar matakan da suka dace wajen warware matsalar tsaro da ake fama da ita a Najeriya.
A cewarsa, ya kamata shugabanni su tsaya su yi aiki domin ci gaban kasar da al’ummarta.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button