Wasu Abubuwan Da Zaki Iya yinsu A Tube Da Mijinki Ba Sai saduwa Ba
Makaranta tsangayar malam wanda Tonga Abdul Tonga ya wallafa a shafinsa wanda karatun na ma’aurata ne wanda ake nunawa mata abubuwan da zasuyi domin mazajensu suji dadi ba dole anyi saduwa aure ba.
Akasarin ma’aurata musamman mata basa iya tubewa a gaban mazajensu su saki jiki. Wasu matan idan har mazansu sun gansu a tube, to Jima’i ne za a yi dasu ko ake yi dasu.
Ga wasu abubuwan da zaki iya yi a gaban mijinki a tube ba sai Jima’i ba.
1: Zaki iya rungumar mijinki a tube zigidir kuna kwance ba tare da kunyi Jima’i ba.
Akasarin Maza suna son matansu su rungumosu a Kwabe. Wannan runguma ba kaya a jikin mace na kara kauna tsakanin ma’aurata.
2: Kina iya yiwa mijinki tausa ba tare da sanya kaya a jikinki ba.
A daidai irin wannan yanayin zaki kwadaitar da mijinki kanki duk kuwa da ba Jima’i zakuyi ba.sai dai hakan na karawa maigida sonki.
3: Sintiri a gaban mijinki tsirara wani tsari ne da mata suke cusawa mazansu soyayyarsu da motsa su.
Ba lalle sai kina da kuturin juyawa ba ko nonuwan kadawa ba. Duk irin yanayin jikinki zai miki tasiri wajen jawo hankalin mijinki.
4: Rausaya, da yin rawa a gaban mijinki tsirara wannan ma yana kwadaitar da mijinki ke. Tare da cusa masa kaunarki.
5: Kwalliya tsirara a gaban mijinki yayin shafa mai ko abunda yayi kama da hakan yanayi ne da maza suke so saboda yadda yake kwantar dasu matansu.
Yanada kyau mata ma’aurata su fahimci cewa, ba dai-dai bane boyewa mijinki jikinki ko tsairaicinki.