Labarai
Zaben da muka yi mun yi kura-kurai – Gwamna Yari
Advertisment
Gwamnan Zamfara mai barin gado Abdulaziz Yari Abubakar ya amince da hukuncin kotun koli tare da yi wa wanda zai gaje shi fatan alheri.
A yayin da yake jagorantar shan ruwan azumin ramadan na karshe tare da kwamishinoni da manyan kushoshin gwamnatinsa a gidansa da ke Talatar Mafara gwamnan ya ce “mun aminta kuma mun yadda da hukuncin Ubangiji.”
Mun samu wannan labari ne daga bbchausa.com A ranar juma’a ne kotun koli ta yanke hukuncin cewa jam’iyyar APC ba ta yi sahihin zaben fitar da gwani ba wanda hakan ya yi sanadin soke kuri’un da jam’iyyar ta samu a dukkanin kujerun da ta lashe a zaben 2019 a jihar.
Hukumar INEC kuma ta tabbatar da ‘yan takarar jam’iyyar PDP da suka zo na biyu a matsayin wadanda suka lashe zaben na gwamna da na ‘yan majalisar Tarayya da na jiha.
Da yake jawabi, Gwamna Yari ya amsa cewa zaben da aka yi akwai kura-kurai a ciki, inda ya ce sun yadda da hukuncin kotun koli, “wannan tsari ne wanda Allah ya riga ya tsara haka.”
“Imanin mutum ba ya cika sai ya yi imani da kaddara alheri ko sharri,”
“Wannan yana cikin sharadin cewa imaninmu ya cika,” in ji shi.
- Zan magance matsalar tsaro a jihar Zamfara – Bello Matawalle
- APC ta fadi zaben jihar Zamfara – Kotun koli
Gwamna Yari ya kuma yi wa gwamnatin da za ta gaje ji addu’ar fatan alheri, inda ya ce yana fatan Allah zai ba su ikon yin adalci.
“Allah ya masu jagora ta hanyar da jihar Zamfara za ta ci gaba da kuma hanyar da al’umma za su ci gaba.”
An ta yada hoton bidiyon jawabin gwamnan a kafofin sada zumunta na intanet.
KALLI WANNAN BIDIYON DOMIN YADDA GUWAYYUN SHEHI SU KA YI SANYI….Posted by Maibiredi Tv on Saturday, 25 May 2019
INEC ta fitar da jerin sunayen zababbun ‘yan takara a Zamfara
Gwamna da mataimaki
12. In compliance with the Supreme Court judgment, the Commission has now determined the winners of the elections in Zamfara State as follows:Governorship
1. GOVERNOR: BELLO MOHAMMED MATAWALLE, MALE, PDP
2. DEPUTY GOVERNOR:
MAHDI ALIYU GUSAU, MALE, PDP.— INEC Nigeria (@inecnigeria) 25 Mayu, 2019
‘Yan majalisar dattawa
Senatorial
1. ZAMFARA NORTH
ALHAJI YA’U SAHABI
MALE, PDP2. ZAMFARA CENTRAL
MOHAMMED HASSAN
MALE, PDP3. ZAMFARA WEST
LAWALI HASSAN ANKA
MALE
PDP— INEC Nigeria (@inecnigeria) 25 Mayu, 2019
‘Yan majalisar Wakilai
House of Representatives
1. KAURAN NAMODA/BIRNIN MAGAJI
UMAR SANI DAN-GALADIMA
MALE, PDP2. SHINKAFI/ZURMI
BELLO HASSAN SHINKAFI
MALE, PDP3. GUSAU/TSAFE
KABIRU AMADU
MALE, PDP4. BUNGUDU/MARU
SHEHU AHMED
MALE, PDP5. ANKA/TALATA MAFARA
KABIRU YAHAYA
MALE, PDP— INEC Nigeria (@inecnigeria) 25 Mayu, 2019
6. BAKURA/MARADUN
AHMED MUHAMMAD BAKURA
MALE, PDP7. GUMMI/BUKKUYUM
SULAIMAN ABUBAKAR GUMI
MALE, PDP— INEC Nigeria (@inecnigeria) 25 Mayu, 2019
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com