Labarai

Bayan Kashe Al’umma Da ‘Yan Bindiga Suka Yi A Yankin Shanga Dake Jihar Kebbi, Sun Sake Dawo Sun Bankawa Wani Kauye Wuta (bidiyo da hotuna)

Advertisment

Bayan Kashe Al'umma Da 'Yan Bindiga Suka Yi A Yankin Shanga Dake Jihar Kebbi, Sun Sake Dawo Sun Bankawa Wani Kauye WutaBayan cikin jimami da radadin zafin rashin da da al’umma ke ciki na rashin rayuwar ‘yan uwansu da ‘yan bindiga suka kashe tare da garkuwa dawani, sun kara garzayowa wani kauye mai suna Tungar Zarumai suka bankawa garin wuta a jiya Asabar.
Dukiyar al’umma da kuma abincinsu duk sun salwanta, yayinda al’ummar kauyen kowa ya tsere domin tsira da rayuwarsu.
Har yanzu dai cikin zancen al’umma wannan yankin suna cikin fargaba a wannan karamar hukumar mulki ta Shanga. Wanda ake duban cewa matukar ba jami’an tsaro suka kawo dauki ba to tabbas zasu Kara aikata wani mummunar ta’adin.
~Yushau Garba Shanga.

Irin yadda talakkawan arewa ke cigaba da dandana kudarsu kenan a hannun makiyan Allah.
Akwai ire Iren TUNGAR ZARUMAI sunfi dubu da yanfashin daji suka Kona tareda kashe mutane da sace wasu domin naiman kudin fansa.
Ina hasashen tabbas Nan gaba kadan Nigeria kancokam ka iya komawa kamar kasar mexico a baya tabbas idan kuwa wannan hasashen ya tabbata to tabbas masu mulki sunyi bankwana da runtsa idanunsu da sunan barci.
Lallai a irin wannan yanayi na kisa da gadara da yan”taadda sukeyiwa al’ummar arewacin Nigeria abun Allah waddaine.
Mustapha sarkin kaya ya wallafa bidiyon a shafinsa na Facebook.

Advertisment








Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button