Labarai

Karin haske akan gawarwakin da ake yadawa na barayin daji da aka kashe

Majiyarmu ta samu cikakken labarin bayan akan gawarwaki da ake yada a soshiyal midiya wanda wasu na son asalin inda abin ya faru da kusan gawa nawa ne dan uwa ma’aboci bibiyar labaran harda tsaro na Najeriya Mustapha sarkin kaya ya ruwaito labarin a shafinsa na sada zumunta.

Watau gaskiyar maganar itace wannan fadan ya farune kusan ince kan iyakar zamfara da kebbi ne, anfaro rikin ne daga kan titin Sageko Malekachi a jahar Kebbi state.

Lokacin da Sojojin Nigeria suka samu bayanen sirri da cewa anga wadannan Yan bindigar masu yawan gaske a kauyen madada ta karamar hukumar maru jahar zamfara ranar Talata 11 Oct 23 da rana.

Karin haske akan gawarwakin da ake yadawa na barayin daji da aka kashe
Karin haske akan gawarwakin da ake yadawa na barayin daji da aka kashe

Daga Nan ne barayin suka nufi jahar ta kebbi da niyyar kaiwa jami’an tsaron hari da Kuma wasu kananan kauyukka.
Amma Kuma suka juyo zuwa kauyen dan gurgu saboda sun samu labarin cewa Sojoji na jiran su a kauyen bena da malekachi.

Haka suka hakura suka koma dajin dan sadau, karamar hukumar maru a jahar zamfara.

Nan nefa jirgin yakin sojan Nigeria na operation hadarin daji dake bin diddigin su barayin ya fara yi masu wannan kissan kiyashin a kauyen dan mani da misalin karfe 01:30 zuwa karfe 02:30, da yayi sanadin kissan wannan gawarwakin da ka gani a na yadawa.

Tabbacin da muka samu ankashe a kalla gawa barayin su100 da yan kai duk da yake gawarwakin sunyi rugu rugu da baza ka iya kirgawaba.

Daga baya Kuma sojojin Nigeria sun sake binsu ta kasa Inda suka sake kashe wasu Karin 17 daga cikin barayin Dake kokarin tserewa.

Sojojin sunyi nasarar kwacewa da kone masuna
17.

Akwai Kuma ingantaccen labarin dake cewa an hangon barayin suna binne ga warwaki masu yawa a rame daya a kauyen sangeko ta jahar Niger da Kuma babban dokata karamar hukumar maru jahar a zamfara ankuma kama waddanda suka ji raunin halbin bindigar a kauyen na babban doka .

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button
DOMIN SAMUN GARABASA