Labarai

Allahu Akbar : Matashin daya rasa ransa bayan sadaukar da kodar sa ga mahaifiyar sa

An ayyana wani dan Najeriya da ba a bayyana sunansa ba a matsayin jarumi bayan ya bayar da kodarsa domin ceto rayuwar mahaifiyarsa. Matashin wanda hotonsa ke yawo a kafafen sada zumunta na zamani cikin jimami ya rasa ransa bayan ya bayar da kodan sa. Labarunhausa na ruwaito

Mahaifiyarsa ta rayu

An bayyana cewa mahaifiyarsa ta rayu daga tiyatar da aka yi mata inda shikuma ya rasa ransa, lamarin dai ya karya zukatan mutane da dama a shafukan sada zumunta.

Masu amfani da Twitter sun mayar da martani

@DanielRegha ya rubuta cewa: “lallai wannan abin tausayi ne Allah ya ba ya huta. Ina mika ta’aziyyata ga masoyansa, tare da yi musu fatan Allah ya masa rahama ita kuwa mahaifiyarsa ina mata fatan samun sauki cikin gaggawa.”

@wifibrain_ yayi sharhi: “Tabbas muna son iyayenmu mata kuma duk wani abu na sadaukarwa da muka yi musu ba zai taba kama soyayyar da suke yi mana ba. Amma sadakar gabobi zunubi ne ga Allah. Kuma na tabbata uwar ba za ta bar shi ya aikata hakan ba in da tasan hukuncin da ya yanke.”

@TeeKay_Kuranga ya ce: “Ni ma zan iya yi wa mahaifiyata haka. Ko da yake mahaifiyata ta rasu, idan aka ce min tana bukatar wani sassan jiki ba zan yi shakkar samar da su ba.”Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button