Labarai

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da satar azzakari a bauchi

Rundunar yan sanda jihar bauchi sunyi nasara kama wani mutum mai suna Joshua yohana da satar azzakari a jihar bauchi da ke arewacin najeriya.

Idan baku manta na a kwanan baya an samu rahotani daga jahohi daban daban wanda wannan al’amari ya dawo na shafi mulera joshua yohana yayi hirar da manema labarai inda yan sanda suke tambayarsa me yayi anka kawo shi a wannan waje ga abinda yake Cewa .

Asalin abinda yasa anka kawo ka a nan?

“Na sace bura ne, magani ne ake shafawa a hannu da kun sha hannu da shi ma’ana da kun gaisa da mutum magana ta kare idan na sace ina baiwa abokina bitrus iliya idan na sace na bashi bansan abinda yake yi da shi ba.”

Yan sanda sun kama wanda ake zargi da satar azzakari a bauchi
Yan sanda sun kama wanda ake zargi da satar azzakari a bauchi

Nawa kuke sayarwa idan kun sace alurar mutum?

“Joshua ni bai fadimin ba kawai idan na sace ina bashi yana kaiwa ogansa amma har yanzu ko sisi bai bani ba, tun ranar lahadi na fara wannan aiki amma wannan shine mutum na farko da na sata kuma anka kamani.

“Joshua yace asalin sana’arsa noma ce, ni ma’auraci ni ina da mata da yara”

Mai tambaya : idan anka sace na yaranka ya zakaji?

“Gaskiya bazanji dadi ba ina da yara hudu da na haifa ”

Mai tambaya : me kake so gwamnati tayi maka ?

“Joshua tayi mini afuwa”

Mai tambaya: yanzu ina azzakarin wanda kunka sace kuma ana mayarwa?

“Joshua eh ana mayarwa amma wanda yake mayarwa ya mutu, shi azzakarin yake hannunsa.”

Mai tambaya: bitrus ina abinda kunka sata?

“Bitrus wancan ne ya da ya sace azzakari ya bani ni kuma na kaiwa oganmu unana Abubakar ya mutu, gaskiya shi mai gidan namu bai gayamuna abinda za’a yi da shi ba.”

Mai tambaya: shin nawa ne zai baku idan kunka cire kuma nawa kunka cire?

“Bitrus gaskiya bamuyi ciniki ba kuma bai gayamuna ko nawa zai bamu ba ya mutu, a lokacin da ya aminta zai mayar domin yana hannunsa shi yasan yadda zai mayar sai yayi kokarin guduwa shinw anka bugeshi da kan bindiga, sai ya fadamusu cewa shi yana hannunsa ya bada lokaci karfe takwas na dare shine kafin lokaci ya mutu.

Mai tambaya shin ana satar na mace?

Bitrus yayi murmushi yace a’a ba’a satar na mace.

Ga bidiyon hirar nan.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button