Dan balki kwamanda yayiwa rarara martani akan kalamansa da yayiwa buhari
Fitaccen dan gwagwarmaya nan abdulmajeed almustapha kwamanda wanda aka fi sani da dan balki kwamanda yayi martani akan irin kalaman da dauda kahutu rarara yayiwa tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.
Wanda shima ya nuna sam baya tare da shi kuma yayi kuskure da zaiyi shekaru aru aru bai gyara wannan kuskure da ya tabka a rayuwarsa, ga abinda yake fadi
“Ranar kunyi fira da rarara wanda bayan gama firar da yan jarida na dauki waya na kirashi nace masa wannan ɓarna da kayiwa kanka zaka dade baka gyara ta ba.
Margayi Dan ladi kamedi shine ya fara fito da rarara daga nan ya hadashi da ruwa baba a lokacin yana algon da ya zamo mataimakin gwamna shi kuma dan Ladi kamedi ya zamo algon sai ya haɗa ruwa baba da rarara shikenan abu yayi ta tafiya sunan rarara bai fara fita ba sai da ya samu buhari.
Ko babu komai ya mutunta shi ,ya girmama shi , ya fito da sunan fiye da na da. Sa’a nan haka rarara kada ya mance shida honourable sha’aban jirgin da shugaban kasa yake hawa anka dauko shi da rarara anka kawo su a nan garin, ko babu komai wannan karamchi ne.
Duk wanda rarara yayiwa waka ya bashi kuɗi albarkacin buhari ne tun daga kan su masari da ganduje kowa albarkachin buhari ne a wancan lokacin.
Sai kuma akan maganarsa cewa daga masari sai Abdullahi Umar ganduje sai shi da yayi waka ya sunfi bada gudunmawa akan tinubu wannan yayi kuskure wadanda sunka bada gudunmawa a siyasance suna da yawa Sa’a nan ka sani siyasa gadon amarya ce -inji dan balki kwamanda
Dan balki kwamanda ya kawo mutane da yawa da sunka taka rawar gani a tafiyar buhari ba’a basu komai ba har shi kansa amma bazasu iya fitowa su fadi irin wannan maganganu ba, saboda akwai tunani da hankali ko ba komai kullum ina fada na godewa Allah ko ba komai dalilin buhari Allah ya daukaka ni na yarda kuma nayi imani da haka naci albarkacin buhari domin duniya a lokacin buhari ta sanni – cewar kwamanda.
Yanzu dan uwana rarara kace idan za’a yi ministoci ko daraktoci ko masu bada shawara sai anyi shawara da kai mutane milliyoyin da suke mafiya ba’a yi shawara da su saboda matsayin ka na mawaki kace ayi shawara da kai, wai koda ministoci biyu a bashi saboda Allah in banda kaji dadin rawar rarara ba kai kadai ne mawaki ba, ya kamata ka dinta tattaunawa maganar da zata zamo maka alkhairi, wannan tabon da yayiwa kansa yana da wahala ya warke .
Kuma nan gaba hatta kashim shettima, Ganduje da tinubu da duk wanda yake jam’iyar Apc bazai yarda da shi ba, saboda abinda yayiwa buhari zai musu- inji dan balki kwamanda.
Ga bidiyon nan domin ku saurari cikakken bayyanin da shi Abdulmajeed almustapha kwamanda ya wallafa a shafin na sada zumunta.