Datti Assalafy yayi Martani zuwa Ga Malam Kabiru Gombe kan Tinubu
A yan kwanakin nan anga bidiyon malam kabiru Gombe inda yake bayyanin halayen ko wane dan takara sai dai ana ganin malam kamar ya nuna banbanci karara inda ya dade yana bayani akan tinubu da yazo kan Atiku yayi dan lokaci kana wanda haka ya zawo marubucin datti Assalafy yayi martani a shafin na sada zumunta ga abinda ya wallafa a Shsfinsa na sada zumunta.
“Kowa Yana Da Nasa Ra’ayin A Siyasa
Lokacin da Malam Sheikh yazo bayani akan alherin Atiku Abubakar sai yayi bayanin a takaice cikin ‘yan dakika, a hakan ma cewa yayi yaji wani ne ya fada, amma da yazo bayani akan Maikarkarwa sai da ya kai kusan mintuna 7, to ban san dalilin da yasa yayi hakan ba
Kuma a alherin Maikarkarwa da Malam yayi bayani babu wani alheri da ya yiwa Musulunci imbanda daukar nauyin ‘yan kabilarsa zuwa aikin hajji da gina musu asibitin jinyar ido, yankin Arewacin Nigeria fa? halaka ‘yan Arewa yayi, ya lalata musu dukiyarsu, ya mayar da matan ‘yan Arewa mazauna jiharsa zawarawa, ya mayar da yaran ‘yan Arewa marayu, ya rushe musu kasuwanni ya kwace musu gidaje
To amma watakila Malam ya manta bai bayyana wa duniya dubban rayukan ‘yan Arewa da Maikarkarwa ya salwantar ba, kuma watakila Malam ya manta da wasiyyar da Malam Ja’afar ya bayar akan Maikarkarwa cewa idan an ganshi a kashe shi, duk da wasiyyar Malam Ja’afar tayi tsauri, bama tare dashi akan wasiyyar, amma hanyar da zamu dauki fansan jinin ‘yan uwan mu da Maikarkarwa ya halaka shine mu guje wa kin zabansa a halin yanzu
Ni kam har ga Allah bana tare da masu ganin Malam ya karbi kwangila daga gurin Maikarkarwa, idan ma ya karba to ina ganin hakan a matsayin nasa lissafin na siyasa, hakan ba zaisa naci mutuncinsa ba, domin ba laifi bane bisa dokar Kasa
Har kwanan yau ana wulakanta ‘yan Arewa a jihar Maikarkarwa, ana musu kamun kaji, yana da ikon ya sa a hana amma ya kawar da kai saboda kabilanci da tsanar da yake yiwa ‘yan Arewa
Amma tabbas a wannan karon ya dace ‘yan Arewa mu hadu mu hukunta Maikarkarwa mu dauki fansar jinin ‘yan uwan mu dubbai da ya salwantar lokacin da yake Gwamna
Yaa Allah Ka haramta wa makiyan mu samun nasara أمين يا حي يا قيوم”