Labarai

Yan bindiga sunyi awon gaba da yan matan amarya biyar ana cikin shagalin biki

Wasu ƴan bindiga sun kutsa kai cikin wani garin da ake kira da Sukola dake a karamar hukumar Bakori ta jihar Katsina a cikin satin da ya gabata inda kuma suka sace wasu mutane shida (6) ciki hadda ƴan matan Amarya su biyar (5).

Majiyar mu ta Premium Times dai ta ruwaito cewa wani mazaunin garin na Sukola da ya nemi a sakaya sunan sa ne ya bayyana hakan

A cewar sa, yan matan Amaryar ba Ƴan garin Sukola din bane amma dai garuruwan su na a kusa da garin kuma sun zo ne domin gudanar da

shagulgulan bikin Amaryar.
Mazaunin Unguwar ya zayyana sunayen matan da aka sace da suka hada da Maryam Sani, Maijidda Kabir, Abida Matthew da Maryam Ibrahim sai kuma ɗayar wadda yace bai san sunan ta ba.

Ya ce Yan bindigar sun shiga garin na Sukola ne da misalin karfe 11 na daren ranar kuma su ka ci karen su ba babbaka kafin daga bisani jami’an yan sanda su iso bayan sun tafi.

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar tsaro ta yan sanda na jihar Katsina dai, ASP Sadiq Abubakar ya tabbatar da aukuwar lamarin inda kuma yace jami’an su na cigaba da bincike.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button