Labarai

Kuncin Rayuwa : Gwamnatin kano ku dubi Allah ku tsayar da wannan ɓarna kuɗi- Abba hikima

Advertisment

Lauyan nan na Kano, Abba Hikima Fagge, ya bukaci Gwamnatin Kano da ta duba Allah ta tsayar da aikin gadojin da ta kuduri aniyar yi a Kano, ta hanyar ɗibar kudaden kananan hukumomi don gina gadoji a birni alhali kauyuka na cikin matsanancin hali da bukatar aiki leadershiphausa na labarto ma majiyarmu labarin.

Abba Hikima ya bayana hakan a shafinsa na Facebook a safiyar ranar Laraba inda mabiyansa ke ci gaba da bayana tsokacinsu kan kalaman nasa.

Hikima ya ce, “Irin wadannan abubuwan da ake dauko wa ke sawa mutane suke daukar gaba daya ashe ‘yan siyasa irinsu daya, ”

Yanzu saboda Allah ina adalci anan? Kauyukan Kano suna cikin mugun hali, kwanaki Freedom Radio ta yi ta bankado matsalolin kauyukanmu amma a dauko kudinsu a saka a gada guda daya Me wannan kudin?”

Lallai akwai wani abu da yake faruwa a kasa.” cewar Abba Hikima.

Kuncin Rayuwa : Gwamnatin kano ku dubi Allah ku tsayar da wannan almubazzaranci - Abba hikima

Mutane sun tofa albarkacin bakinsu akan wannan maganar da abba hikima yayi.

@Abdulaziz abdulaziz cewa yake :

Lokacin da na ga sanarwar gina waɗannan gadoji na yiwa wasu abokai na guda biyu personal message (saboda gudun magana publicly ƴan baka su maida abin siyasa). Abinda na rubuta musu shi ne idan har mun ta sukar Ganduje akan misplacement of priority wajen kashe maƙudan kuɗaɗe don gina gadoji alhali akwai more pressing needs ban ga dalilin yin shiru akan gadar Tal’udu da sauran da Abba yake shirin yi ba.

@nanerh hawwerh cewa take ; Magana Gaskiya, ni kai na bana goyon bayan wannan aikin, akwai kauyuka da suke da bukata fiye da wannan aikin, Don Allah mahunkunta su duba wannan al’amari. Abba Kabir Yusuf.

Allah Ya Tabbatarwa Da Abba Nasara A Supreme court Alfarmar Annabi S.A.W.

@Aminu isah cewa yake: Malam Abba Hikima namu, Yanzu gani kake kamar kaine Madugu sai abunda yayi maka ko ka fahimta za ayi.

Alhamdulillah wannan ma chigaba ne tunda gashi an gayawa mutane inda kudin su zaije sabanin lokachin Barayi sai dai kawai kuji shiru sun kwashe kudaden.

Alllah ya taimaki H.E Abba Kabir Yusuf ya bashi nasara a Supreme Court.

@Musa L maje cewa yake: Duk kananan hukumomin wajen garin Kano ba inda babu matsalar hanya. I am from Sumaila, hanyar da ta tashi daga garin Sumaila har zuwa iyakar mu da Bauchi, ta keta ta fiyeda mazabu takwas, babu titi kuma bata biyu wa a lokacin damuna, tsabar lalacewa tsawon shekaru, hakan ya gurgunta kananan yan kasuwa masu cin kasuwannin kauye.

Hanyar bela itama a karamar hukumar ungoggo duk irin muhimmancin ta, mutane da yawa sheda ne akan irin wahalar da ake sha a sakamakon lalacewar hanyar, kuma gwamnati batada wani tanadi akai, da dai sauran su.

Ana wannan halin kuma ace za’a debi kudaden kananan hukumomi har billion sha daya domin aikin hanya a Dan’agundi sam babu technology kuma an shiga hakkin al’umma.

Nima yau nace Gawuna is coming, kuma ina fatan idan yazo zaiyi adalci akan wannan danyen hukuncin, banida sauran faith a gwamnatin Abba.

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Advertisment
Back to top button