Addini

Sheikh lawan Abubakar Triumph yayiwa shirin ‘Mata A yau’ na Arewa24 Tv wankin babban bargo

Advertisment

A cikin satin da ya gabada har zuwa yanzu mutane suna tofa albarkacin bakinsu akan wannan shiri na MATA A YAU da talabijin din arewa24 tv ke gabatarwa inda cikin shirin daya daga cikin masu shirin ta kawo wani babban al’amari wanda sam bai dace ba tana yar musulmi amma ta kawo wannan zancen akan wai “miji ne zai saki Matarsa saboda bata gaishe shi” a nasu tunanin ya nuna cewa wannan sam bai dace ba kuma wai shirin na fadakar da mata zaman aure ne.

Sheikh lawan Abubakar Triumph yayi tsokaci akan wannan shiri da tashar keyi inda yake cewa.

Yanzu akwai wani lalatacen shiri da akeyi a wata tasha wai “Mata A Yau” billahilazi idan anka cigaba da wannan shiri adadin zawarawa a kasar hausa zai karu kuma bincikenmu ya tabbatar wallahi da gayya anka kawo shi, duk wanda yake mu’amala da wannan gidan tv zai gayamaka shiri biyu sunka fi baiwa muhimmanci , shiri na farko shina wannan hiphop din zafafa goma 10.

Shi kuma ajenda ce ta alala ta mana samari dan haddan Qur’anin da suke yi su dena karatun bokon da ya dan rage mana aka mana rata ya watse yaran mu su koma fitsarararu marasa kunya su zama masu zazaɓo wando kasa alama ta yan neman maza wannan shine ajanda duk mutumin da ya zamo bako a wannan shirin kyauta da ake masa ta musamman ce. Wato shiri na biyu na lalacewa shirin “Mata a yau”.

Ba cewa muke su masu gabatar da shirin lalatatu bane amma muna haska musu su basu masan ajanda da aka shirya ba aiki ake da su sani ba, kaga mace tazo ta saki kalma, kalma da babu ladabi ko ga Allah ya ma za’a ce ayiwa mace kaza to wa kike gayawa Allahn da yayi ta! yanzu Allah kikewa gyara ko Annabi da yazo da shiriya shikikewa gyara mutanen da dukkansu idan kasa musu ahalari ba bazasu iya fassara maka shi ba.

Amma zakaji suna fatawa ae ko addini bai ce kaza ba to wane addini! abin tambaya shin wane addinin kuma har yau wani abu da mutane basa ganewa bahaushe yayi hikimar zance duk wanda zai baka riga ka kalli ta wuyansa.yanzu ace bazawara da taki zaman aure ita zata zo ta koyar da zaman aure in fitsari banza ne kaza tayi mana.

Ko kuma rikakiyar budurwa da bata samu miji ba balantana ma ta shiga tasan duniyar ita zata zo ta koyar da aure? ko kuma tsohuwar da batasan mutuncin kanta da kimar kanta ba, kina tsohuwa yar shekara kaza ki fito da janbaki da jagira a tv kina waska ne wai ke zaki koyar da zaman aure amma wane irin zaman aure zaki koyarwa.”

Advertisment






Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button