Tsohon Ministan Sadarwa da Tattalin Arziki a Fannin Fasaha, Isa Ali Pantami, ya bayyana cewa rasuwar Sheikh Abubakar Abdullahi Giro ta girgiza shi.
A wani sakon ta’aziyya da ya wallafa a shafinsa na facebook, Pantami ya suffanta rasuwar ta Sheikh Giro a matsayin mai raɗaɗi.
“Yanzu na samu labarin rasuwar Sheikh Abubakar Giro Argungu. Hakika irin wannan mutuwa tana da zafi sosai, amma mun tabbata Allah ba ya yin kuskure.
“Don haka muna mika ta’aziyyarmu ga iyalansa, dalibansa, da shugabannin addinin Musulunci a fadin kasar nan.
“Muna addu’ar Allah ya gafarta masa kurakuransa, ya kuma ba shi zaman lafiya,” in ji Mista Pantami a shafinsa na Facebook.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa malamin, wanda ya fito daga garin Argungu na jihar Kebbi ya rasu ne bayan gajeruwar rashin lafiya a jiya Laraba.
Rahotanni sun ce Giro ya kamu da rashin lafiya jim kadan bayan ya yi wa’azi a wani masallaci da ke Birnin Kebbi a ranar Talata.
A wani sako da kungiyar Jama’atu Izalatul Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah, JIBWIS ta wallafa a shafinta na Facebook, ta ce za a yi jana’izar babban malamin a yau Alhamis karfe 2:30pm a cikin garin argungu.