Addini

Mutum ne ya turawa matarsa saki ta WhatsApp kafin ta bude sai ya goge,ita kuma tana amfani da “Gbwhatsapp” sai tagani sakin ya yiyu? – Dr. Bashir Aliyu Umar

Mutum ne ya turawa matarsa saki ta manhajar WhatsApp wanda shi yana amfani da asalin WhatsApp ne yayinda ita matar take amfani da wanda yake na bayan fage ne wanda ake kira “Gbwhatsapp” sai ya goge sako a daidai lokacin da ita matar bata buɗe sakon ba.

Amma bisa rashin sa’a ita matar tana amfani da manhajar “Gbwhatsapp” Wanda idan anka turo sako kana gani shin dan Allah malam minene hukunci?

Amsa

“To fah tunda ya riga ya turamata , a daukama ya turamata bata gani ba sai daga baya yazo ya goge wanda yana bada damar goge min ko gogewa kowa,amma wannan bai kore ta gani ba.

Mutum ne ya turawa matarsa saki ta WhatsApp kafin ta bude sai ya goge,ita kuma tana amfani da "Gbwhatsapp" sai tagani sakin ya yiyu? - Dr. Bashir Aliyu Umar
Mutum ne ya turawa matarsa saki ta WhatsApp kafin ta bude sai ya goge,ita kuma tana amfani da “Gbwhatsapp” sai tagani sakin ya yiyu? – Dr. Bashir Aliyu Umar

Ai tunda dai ya rika ya tura shikenan saki ya afku sakin yayi”.- inji Dr bashir.

Malam ya kara da cewa a mashabar imam malik idan mutum ya rubuta saki ko yaje ga matarsa yana tunanin sai yayi shawara to idan har matar taga sakin a rubuce to sakin ya afku ma’ana sakin yayi, amma idan bata gani ba sakin bai afku ba ma’ana sakin baiyi ba idan ya dawo daga baya ya goge rubutun ko ya goge takarda shikenan matarsa na nan.

“Dan haka duk wanda ya turawa Matarsa saki ta hanyar sms ko WhatsApp ko yaje ko bai je ba sakin ya afku, saboda ya riga yayi azama yin sakin din”

Shafin Dr. Bashir Aliyu umar ne suka wallafa wannan bidiyon fatarar.

Ga bidiyon nan

Mr HausaLoaded

Abubakar Rabiu Editor-in-cheif

Related Articles

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Back to top button