Rarara yayiwa talakawa hadarin ruwan abinci da nairori a garin Kahutu (hotuna)
Rarara ya ƙara tallafawa mutane 1,755 da abinci dana cefane a garin Kahutu da ke jiha Katsina
Labari da ya samu majiyarmu mai dadi daga shafin mataimaki na musamman a kafafen sada zumunta Rabi’u Garba Gaya ya wallafa wannan tallafin da babban mawakin siyasa a Nijeriya yayiwa al’umma cikin wannan yanayin talauci da fatara da ake ciki.
Wannan ba shine karo na farko ba da mawakin yake tallafawa jama’ar garinsa ba ko kwanan baya mun kawo muku labarin a cikin hotuna da ya tallafa musu da abinci da kudi.
“Yau Cikin Yaddar Allah, Mai Girma Shugaban Kasar Mawaka Alhaji Dauda Kahutu Rarara Ya Kara Tallafawa Mutane 1,755 Da Kayan Abinchi Da Kudin Chefane A Garin Kahutu Dake Karamar Hukumar Danja, Jahar Katsina.
Al-Ummar Kahutu Sunyiwa Mai Girma Shugaban Kasar Mawaka Alhaji Dauda Kahutu Rarara Godiya Tare Da Addu’ar Allah Ya Jikan Mahaifinsa Mallam Adamu, Sannan Kuma Sunyi Masa Fatan Allah Ya Rabashi Da Mahaifiyarsa Lafiya.”