Mun Nema Alfarma, Za’a Saki Murja Kunya yau Zuwa gobe – injiTeema Makamashi
A yau din nan mun samu wani labari akan fitacciyar yar tiktok murja Ibrahim kunya wanda anka kai gidan gyran hali akan irin bidiyon da tayi akan irin rashin nuna kunya da zage zage kamar yadda ake zarginta shine ake tunanin za’a sake ta kamar yadda nasara radio sunka ruwaito.
Jaruma masana’antar shirya finafinan Hausa ta Kannywood, Teema Makamashi, tace ta nemi alfarma a wajen wandanda ta ke da sanayya dasu, akan batun Jarumar barkwanci ta shafin TikTok, Murja Ibrahim Kunya, wacce ke gidan gyaran hali a yanzu.
Teema Makamashi ta bayyana haka cikin bidiyon da tayi a shafin TikTok, inda ta ce a gobe za’a saki Murja, sai dai idan an samu tsaiko ne za ta kai zuwa jibi.
Sai dai kuma, Teeman ta jaddada cewa, tabbas Murja tayi kuskure bisa abubuwan da ta ke aikatawa a shafukan yanar gizo, amma dai alfarma ce suka nema akan a sake ta.
Ana zargin Murja ne da yada kalaman batsa, zage-zage da kuma rashin tarbiyya, musamman a shafin TikTok, wanda zai kawo cikas ga tarbiyyar addinin musulunci.