Kannywood
An saka Kalmar ‘Kannywood’ a Kamus din Turanci OED
Advertisment
Daga yanzu kalmar Kannywood da ake amfani da ita wajen bayyana farfajiyar fina-finan Hausa ya zama kalmar Turanci.
Madogara : premiumtimeshausa
Ita dai kalmar Kannywood ta samo asali ne a jihar Kano.
Jihar Kano ita ce cibiyar shirya fina-finan Hausa na zamani da hakan ya sa aka yi koyi da takwarar farfajiyar dake kudu wato Nollywood, aka rada wa farfajiyar ta Hausa suna Kannywood.
Wannan kalma ta samu karbuwa a wajen masu shirya fina-finan Hausa da masu kallo. Yanzu dai an saka Kalmar a cikin babban Kamus din Kalmomi ta duniya da ake kira ‘Oxford English Dictionary’.
Baya ga Kannywood, akwai wasu Kalmomi da ake amfani da su a kasarnan da suka samu shiga cikin kamus din OED da suka hada da Okada, da ake kiran masu haya da babur.
Ga sauran Kalmomin:
Agric, adj. & n.
Barbing salon, n.
Buka, n.
Bukateria, n.
Chop, v./6
Chop-chop, n./2
Danfo, n.
To eat money, in eat, v.
Ember months, n.
Flag-off, n.
To flag off in flag, v.
Gist, n./3
Gist, v./2
Guber, adj.
Kannywood, n.
K-leg, n.
Mama put, n.
Next tomorrow, n. & adv.
Non-indigene, adj. & n.
Okada, n.
To put to bed, in put, v.
Qualitative, adj.
To rub minds (together) in rub, v./1
Sef, adv.
Send-forth, n.
Severally, adv.
Tokunbo, adj.
Zone, v.
Zoning, n.
Mun Dauko Daga Shafin Hausaloaded.com