Ramadan: Zan taimaka wa mutane sama da 5,000 a wannan wata – Rasheeda Maisa’a
FITACCIYAR jaruma Rasheeda Adamu Abdullahi (Maisa’a) ta bayyana cewa ta na san za ta tallafa wa mabuƙata sama da 5,000 da kayan abinci a wannan wata na Ramadan.
Ta yi wannan bayanin ne ga mujallar Fim jiya, jim kaɗan bayan da ta fara rabon kayan azumi wanda gidauniyar ta mai suna ‘Maisa’a Charity’ ta saba bayarwa ga mabuƙata da marayu har ma da naƙasassu a kowace shekara.
Kamar yadda mujallar fim na ruwaito Jarumar, wadda kuma sananniyar ‘yar siyasa ce, ta yi fice wajen agaza wa marayu da sauran mabuƙata tsawon shekara tara, inda a ƙarƙashin gidauniyar ta mabuƙata sama da 400 su ka samu tallafin kayayyakin abinci domin yin amfani da su a cikin wannan watan na Ramadan.
A zantawar ta da mujallar Fim, Rasheeda ta ce, ‘’Cikin yardar Ubangiji, tuni wannan gidauniyar ta fara aiwatar da aikin ta wanda tun azumi ya rage saura kwana biyu mu ka samu damar fara ɗaukar sunayen mutane wanda ba mu ma sanar da su me za mu yi musu ba, amma dai mun bi guri-guri mun ɗauki sunayen irin waɗannan mabuƙata wanda a yanzu haka mun ba wa duk wanda mu ka ɗauki sunan sa tallafin kayan, cikin yardar Allah.
“Sannan akwai tsarin da shi ma in-sha Allahu za mu gabatar nan gaba, na bi gida-gida domin ba wa mutanen da ke buƙata.’’
Shin a ina Rasheeda ke samun tallafin da ta ke raba wa jama’a? Amsar ta ita ce: “A wannan gidauniyar tawa mu na samun tallafi daga hannayen mutane daban-daban, wanda ya haɗa da manya-manyan ‘yan kasuwa da masu hannu da shuni, manya-manyan kamfaninnika da hukumomi har ma da gwamnati.
“Wannan kayan da mu ka fara rabawa ya zo ne daga wurin Maiɗakin Shugaban Ƙasa, A’isha Buhari, a ƙarƙashin tsarin nan na ‘Future Assured’ wanda ko da ba azumi ba idan wata hidima ta taso ta kan kira mu ta ba mu tallafi domin a bai wa al’umma mabuƙata.”
Da ta ke kwatanta yadda su ka rarraba kayan tallafi a shekarar 2020 lokacin da aka yi zaman gida sakamakon ɓullar cutar Korona, Hajiya Maisa’a ta ce, “Mun rarraba kaya sama da tirela uku wanda kuma mu ke sa ran a wannan shekarar za mu raba kaya fiye da na shekarar da ta gabata, inda a wancan lokacin mutane da su ke a halin zaman gida sun amfana da tallafin da mu ka ba su, kama daga mutanen ƙauye zuwa na karkara, naƙasassu da sauran su duk sun amfana da wannan tallafi, inda kuma a wannan shekarar ma mu ke sa ran mutanen da za su amfana su fi na wancan lokacin.”
Jarumar kuma babbar furodusar, ta bai abokan aikin ta da ke masana’antar Kannywood da ma sauran jama’a shawara da cewa, “Ina kira ga ‘yan’uwa na da abokanan sana’a ta da kowa ya daure su dinga irin waɗannan abubuwan da mu ke yi na tallafa wa al’umma domin su su ke riƙe da mu. Duk mutumin da ya ciyar da wani ko ba a lokacin azumi ba ya na da lada ballantana a lokacin azumi, wanda ya kamata jama’a ya na ƙoƙarin yage wani abu daga cikin dukiyar sa ya na taimaka wa al’umma kamar yadda mu ke yi.
“Allah ya sa wannan abu da mu ke yi ya sa mana shi a cikin mizanin mu.
“Sannan mu na kira ga masu kuɗi da ‘yan kasuwa da su rinƙa taimaka mana, saboda hannu da yawa an ce maganin ƙazamar miya. A taimaka daga irin ni’ima da arzikin da Allah ya yi musu.”
Kayayyakin da gidauniyar ta raba dai sun haɗa da shinkafa, makaroni, taliya da sauran kayayyakin masarufi na amfanin yau da kullum.